Connect with us

Labarai

NDLEA ta bukaci jam’iyyun siyasa su rinka yi wa ‘yan siyasa gwajin shaye-shaye kafin takara

Published

on

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Buba Marwa ya bukaci jam’iyyun siyasa da su sanya gwajin maganin a matsayin wani bangare na tantance masu neman tikitin takara a shekarar 2023.

Marwa ya yi magana ne a ranar Laraba a shelkwatar hukumar da ke Abuja.

Janar mai ritaya ya ce, ya dade yana ba da shawarar a yi wa masu rike da mukamai da masu neman mukamai gwajin sahye-sahye.

Marwa ya lura cewa, ofishin gwamnati yana buƙatar nauyi mai yawa, kuma ya zama dole a tabbatar da cewa masu rike da su ba su da jaraba.

Shugaban ya ce, irin wadannan mutane na iya amfani da kudin gwamnati wajen shan hodar iblis da sauran miyagun kwayoyi.

“Mutum ba zai kasance cikin kwanciyar hankali ba, don tafiyar da al’amuran da aka damka masa.

“Mun ba da shawarar kuma za mu ci gaba da ba da shawarar cewa, a gudanar da gwajin magunguna ga ‘yan siyasa. Tuni dai wasu gwamnatocin jahohi kamar Kano su ke yin haka.

“Ba ‘yan siyasa kadai ba, har ma wadanda gwamnati ta nada. A safiyar yau na aika wasika zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa.”

Labarai

Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Published

on

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9

Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Published

on

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.

Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Babban Labari: Mun kama mota makare da kayan fashewa da bindugu da harsashi a Kano – Kiyawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata mota makare da wasu kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da kuma bindigu kirar AK47 .

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, sun samu nasarar kama motar kirar Mercedez a unguwar Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.

A cewar Kiyawa sun sami rahoran sirri ne akan motar wadda suke zargin an kawo ta daga Jihar Jigawa zuwa Kano makare da irin kayayyakin da suke zargin da sune ake hada abubuwan fashewa domin aikata ta’addanci.

Sanarwar ta kuma ce bayan samun rahotan sirri na kara sowar motar zuwa Kano, jami’an tsaron Puff Adder suka yi wa mator kawanya, wanda hakan yasa mutanan ciki suka tsere suka bar motar a nan.

“Mun samu nasarar gano bindiga kirar AK47 guda biyu da kuma kananan bindigu biyu kirar Pistol tare da alburusai dubu daya da dari takwas”. In ji Kiyawa.

Continue Reading

Trending