Hukumomi a Saudiyya sun bayyana cewa, mahajjata fiye da miliyan biyu ne suka yi Qiyamul Layli a Masallacin Harami.
Shafin intanet na Haramain Sharifain ne ya bayyana haka shafukan sada zumunta.
“Mahajjata da masu ziyara fiye da miliyan biyu ne suka yi tsaiwar Qiyam Al Layl Prayers a Masjid Al Haram, Makkah a daren 27 na watan Ramadan,” in ji sakon.
Mahajjata da ma sauran Musulmai dai suna sa ran dacewa da Daren Laylatul Qadri a irin wadannan dararen 21, 23, 25, 27, da kuma 29.
Dubban Musulmai ne suka shiga kasar ta Saudiyya a bana domin aikin Umrar, bayan kasar ta sassauta dokokin cutar korona.