Connect with us

Labarai

Sharudan da kotu ta gindaya domin bayar da belin Muhuyi Magajai

Published

on

An gurfanar da tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado, da karfe 12:15 na ranar Juma’a a gaban kotun Majistiri mai lamba 58 da ke zamanta a unguwar No-man’s-land a karamar hukumar Fagge Karkashin mai Shari’a Aminu Gabari.

An karnta masa tuhuma bayar da labarin karya game da batun rashin lafiya da ya ce ya na fama da ita, lokacin ya musanta. Lauyan muhuyin Muhammad, Dan Azumi, ya nemi a sanya shi a hannun beli la’akara da kundin tsarin mulki da ya ce, wanda a ke tuhuma ba mai laifi ba ne, har sai shaidu sun tabbatar, domin hakan suka roki kotun ta bayar da Muhuyi beli.

Sai dai lauyan gwamnati Wada A Wada, ya bukaci kotun da ta yi abunda ya kamata a tsarin shari’a, wajen amsa rokon belin Muhuyi ko akasin hakan, domin akwai yuwuwar Muhuyin ya tsere idan a ka bada Belin na sa.

Da ya ke kwarya-kwaryar hukunci mai shari’a, Aminu Gabari, ya sanya Barisata Muhuyi Magaji Rimin Gado a hannun Beli, bisa sharudan kudi dubu Dari Biyar da kuma shaidar biyan haraji na shekara uku da mutun biyu cikinsu ya zama akwai mahaifin Muhuyi ko limamin massllacin juma’a na Sharada ko Ja’en ko kuma Dagacin Sharada, sannan zai bada Fasfo tare da sanyawa bakinsa takunkumin yin magana a rediyo ko shafin sada zumunta, har sai an gama shari’ar.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa, an kuma dage zaman shari’ar zuwa 04 ga watan Mayu na shekarar 2022.

Labarai

Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Published

on

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9

Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Published

on

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.

Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Babban Labari: Mun kama mota makare da kayan fashewa da bindugu da harsashi a Kano – Kiyawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata mota makare da wasu kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da kuma bindigu kirar AK47 .

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, sun samu nasarar kama motar kirar Mercedez a unguwar Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.

A cewar Kiyawa sun sami rahoran sirri ne akan motar wadda suke zargin an kawo ta daga Jihar Jigawa zuwa Kano makare da irin kayayyakin da suke zargin da sune ake hada abubuwan fashewa domin aikata ta’addanci.

Sanarwar ta kuma ce bayan samun rahotan sirri na kara sowar motar zuwa Kano, jami’an tsaron Puff Adder suka yi wa mator kawanya, wanda hakan yasa mutanan ciki suka tsere suka bar motar a nan.

“Mun samu nasarar gano bindiga kirar AK47 guda biyu da kuma kananan bindigu biyu kirar Pistol tare da alburusai dubu daya da dari takwas”. In ji Kiyawa.

Continue Reading

Trending