Ilimi
ASUU ta ƙara tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU, ta kara tsawaita yajin aikin da take yi da makonni 12.
ASUU ta dauki matakin ne a wani taron gaggawa na majalisar zartarwarta ta ƙasa da ta yi a sakatariyar ta a Abuja.
Taron gaggawar, wanda ya samu halartar manyan shugabannin reshen ta, an fara shi ne a ranar Lahadi kuma ya ƙare da sanyin safiyar Litinin.
Yajin aikin na watanni biyu da kungiyar ASUU ta ayyana ranar 14 ga Maris, 2022, ya kawo karshe a yau 9 ga watan Mayu, don haka hukumar ta NEC ta ga bukatar kara wa’adin makonni 12 bayan fara yajin aikin sai baba-ta-gani, saboda gaza magance matsalolin da ake takaddama a kai.
Ma’anar tsawaita yajin aikin shi ne, jami’o’in gwamnati za su kasance a rufe.
Ilimi
Ciyar da dalibai: Gwamnati ta bayar da horo ga masu dafa abinci

A ranar Talata ne ma’aikatar jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban jama’a ta tarayya, ta horas da masu sayar da abinci 50 a kan tsafta a karkashin shirinta na ciyar da Makarantun.
Shugabar tawagar masu bayar da horo a jihar Naija, Fatima Bissalla, ta ce sun gudanar da wannan horon ne domin baiwa masu sayar da abinci da ilimin da ake bukata kan yadda za su iya kula da tsaftar jikinsu da abinci da kuma yanayin girki, domin amfanin daliban.
“Na yi imanin cewa tsaftar da masu dafa abinci ke yi zai dakile barkewar cututtuka a tsakanin wadanda suka ci gajiyar shirin,” in ji ta.
Ta kara da cewa an bada horon ne, domin tabbatar da cewa, duk dan kwangila, sun rungumi tsaftar muhalli bisa, ka’idar da ma’aikatar ta gindaya musu na su bi tsarin.
Bisallah ta ce, wadanda suka samu horon za su koma kananan hukumominsu, sannan su sauke horon ga sauran masu dafa abinci, ta kara da cewa, jami’an teburi da masu kula da abinci mai gina jiki za su rinka lura da su a yankunan kansilolin.
Har ila yau, Umar Shaba, Manajan Shirye-Shirye na shirin ciyar da Makarantun da ake nomawa a Naija, ya ce, horon ya kara nuna masu yadda dafa abinci irin na tsafta.
Ilimi
Ganduje ya mika sakon ta’aziyar sa ga iyalan Malaman da suka mutu a hanyar Sumaila

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Lahadin ya jajantawa iyalan malaman addinin Islama guda shida da suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su yayin da suke dawowa daga karamar hukumar Sumaila kwanan nan.
“Mutuwar wadannan mutanen ba babban rashi ne ga iyalansu kadai ba, har ma ga jihar baki daya. Abin takaici ne,” inji shi.
“Mun samu labarin cewa Malaman da Sheikh Alkassim Zakariyya ya jagoranta sun fara ziyarar aiki karkashin inuwar Imam Malik Islamic Foundation.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran Abba Anwar ya rabawa manema labarai, ya ruwaito Gwamna Ganduje yana cewa: “Jahar mu ta yi asarar mutane masu tsoron Allah, daga cikinsu akwai Sheikh Alkassim, Malam Isiya Tela, Mustapha Musa Sa’ad, Malam Ishaq, Rummawa da Malam Zakariyya Alkassim Dataka. Allah Ya gafarta musu,” inji shi.
Ilimi
Limamai Ku daina tsawwala a sallar dare ta Tahajjud – Saudiyya

Ma’aikatar Harkokin Addini ta Saudiyya ta jaddada wa limamai a masallatan ƙasar da ke jan sallar dare ta tahajjud da su daina tsawaita addu’o’in Al-ƙunutu don sauƙaƙa wa masallata, a cewar rahoton Saudi Gazette.
Rahoton ya ce, an nemi limaman su kammala sallar da wuri kafin kiran sallar asuba don mutane su samu isasshen lokaci tsakanin sallolin biyu.
Musulmai na yin sallar tahajjud ne da tsakar dare a kwana 10 na ƙarshen watan Ramadana. A yau Asabar ake cika kwana na 15 da fara azumin na Ramadana, wanda Musulamai za su shafe kwana 29 ko 30 suna yi.
Kazalika, ma’aikatar ta umarci dukkan masallatai su yi aiki da koyarwar Annabi Muhammadu S.A.W. game da addu’ar da aka rawaito yana yi yayin addu’ar Ƙunutu.
“Ma’aikatar ta nemi limamai su guji tsawaita addu’o’i har ma su mayar da su matsayin huɗuba. Kuma ya kamata su guji zuzuta murya da kuma yin ƙafiya, ana so su yi addu’a cikin ƙanƙan-da-kai da kuma tawalu’u,” in ji rahoton a cewar BBC.
-
Nishadi2 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai2 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai2 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai2 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Manyan Labarai2 years ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari