Connect with us

Manyan Labarai

Labarai a Takaice na yau 16-04-2019

Published

on

Wani Malami a tsangayar sashen tarihi da hulda da kasashen waje a jami’ar Yusuf Maitama Sule dake Kano, Malam Murtala Mustapha, ya yi kira ga matasa cewa da su tashi tsaye wajen rungumar al’adun Hausa maimakon aron na Bature ko wani Yare.

Malam Murtala Mustapha, ya bayyana hakan ne yayin wani taro na musamman da Jami’ar ta shirya a kan abubuwan da suka shafi Kano tin daga zamanin Bagauda har zuwa yanzu.

Ya ce “cigaban da jihar Kano ta bayar a nahiyar Afrika ya ta’allaka ne ta hanyar bunkasa al’adun Hausa”, sannan kuma ya bukaci matasa dasu tashi tsaye wurin neman illimi don tsiratar da rayuwar su.

Kungiyar bunkasa illimi da cigaban demokradiyya da samar da daidaito a zamantakewa SEDSAC, tarayya bisa matakin da ta dauka na tura jami’an soji a jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna bisa rikicin da yankunan ke fama da su musamman ma masu garkuwa da mutane.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai kunshe da sa hannun babban Daraktan kungiyar, Kwamrade Hamisu Kofar Na’isa ya sanyawa hannu, ya ce “rashin samar da tsaro babban kalubale ne a fadin kasar nan bisa yadda masu garkuwa ke amfani da mugan makamai a hannun su”.

Kakakin hukumar dake kula da gidajen yari na jihar Kano, DSP Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce “Kofar hukumar a bude ta ke wurin tallafawa daurarru musamman a watan Azumin Ramadan mai karatowa”.

yayin zantawarsa jim kadan bayan kammala shirin Shari’a a aikace na gidan Rediyon Dala, DSP Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce “gidan yari kaddara ce ke kai mutum a don haka mutane su guji kyamatar daurarru wanda kowa zai iya tsintar kansa a wannan wuri.

Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi gwamnatin jiha da ta fara amfani da wurin sauke kaya da gwamnatin tarayya ta tanada a yankin Zawachiki dake karamar hukumar Kumbotso.

Kiran ya biyo bayan amince da rahoton hadin gwiwa da shugaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar, Abubakar Zakari Muhammad, ya gabatar a kan dalilan dake kawo cinkoson manyan motocin dakon kaya a cikin kwaryar birnin Kano insa yace masu kayan ba sa kiyayewa da dokokin daukar kayan da hukumar Kwastan ta gindaya masu.

Majalisar dokokin jihar Kano, ta amince da rahoton da kwamatin kula da harkoki addini ya ganatar mata a kan kudirin dokar gyara sashi na 27 na kundin dokar da ta kafa hukumar Shari’a ta jiha ta shekarar 2002.

Shugaban majalisa, Kabiru Alhassan Rurum ne, ya bayyana hakan a yin zaman majalisar da ta yi.

Dan majalisar tarayya ai wakiltar Kunci da Tsanyawa, Injiniya Sani Bala Tsanyawa, ya bayyana cewa karanci wutar lantarki da ake fuskanta a jihar , ya na da nasabane da matsalar saka babban injin Taransifoma a daya daga cikin manyan tashoshin raba wuta dake karamar hukumar Kumbotso Wanda har yanzu ba’a kammala aikin.

Da yake zantawa da gidan Rediyon Dala, injiya Sani Bala ya ce a ziyarar da suka kai tashoshin raba wuta dake Jaba da Sharoro da Kayanji su na da karfin bada wuta sama da abinfa ake bukata, wanda hukumar rarraba wutar lantarki ta kasa itace har yanzu ba ta samar da wutar ga KEDCO ba.

Za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a cikin labaran da muke kawo muku a cikin wannn shafi.

Manyan Labarai

Bamu da wata alaƙa akan dakatar da Ganduje daga jam’iyyar APC – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce basu da wata alaƙa da rikicin cikin gidan da ya kunno kai akan dakatar da Ganduje daga cikin jam’iyyar APC, a Kano.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM a yau Laraba.

Ya ce zargin da jam’iyyar APCn Kano ta yi a kan gwamnatin Kano, kan cewar tana da hannu akan dakatar da shugaban ta na riƙo a matakin ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, zargin bashi da tushe ballantana makama.

A baya-bayan nan ne dai wani sashi na shugabancin jam’iyyar APC, a mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, ya bayyana dakatar da Abdullahi Ganduje daga cikin jam’iyyar.

Sai dai daga bisani shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar ya musanta batun dakatarwar inda ya ce ana shirin ɗaukar matakin da ya dace akan wanda ya fitar da sanarwar.

Bature, ya kuma ce lamarin rikici ne na cikin gidan jam’iyyar ta APC, wanda ya kamata su tsaya su gyara, mai-makon mayar da hankali akan gwamnatin Kano, lamarin da ba za suyi nasara ba.

“Tsagin jam’iyyar APCn, Kano suje can kada su ƙara tsomo mu a cikin rikicin su domin bamu da alaƙa da wani rikicin su ko wani abu, “in ji Sunusi”.

Ya kuma ce ko da yaushe jam’iyyar NNPP, mai mulki a jihar Kano burin su shine ci gaba da taimakawa al’ummar jihar ta hanyar damar da ayyukan ci gaban su.

Dawakin Tofa, ya kuma ƙara da cewa Ganduje bashi da tasiri ko da a ƙaramar hukumar sa ballantana kuma azo batun jahar Kano.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Manyan Labarai

Jam’iyyar NNPP ta dakatar da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf

Published

on

Tsagin jam’iyyar NNPP ta ƙasa karkashin jagorancin Major Agbo, ya sanar da dakatar da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf daga cikin jam’iyyar.

A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar ta ƙasa Ogini Olaposi, ya fitar a yayin taron ‘yan jarida a Talatar nan a Abuja, tsagin jam’iyyar ta NNPP, ya ce rashin bayyana a gaban kwamitin ladabtarwar jam’iyyar da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi shine ya sanya su ɗaukar wannan mataki.

Ya ƙara da cewa matakin na zuwa ne sakamakon fusata da jam’iyyar ta yi kan halartar wani babban taron jam’iyyar da gwamnan ya yi wanda tsagin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya jagoranta a ranar 6 ga watan Afrilun nan na shekarar 2024. kamar yadda jaridar THE PUNCH ta rawaito.

Sai dai tuni wasu ƴan Kwankwasiyyar suka yi watsi da wannan dakatarwa.

Dambarwar dai na zuwa ne yayin da itama jam’iyyar APC, ke ci gaba da fuskantar ta ta dambarwar, musamman ma da aka jiyo yadda wani sashi na shugabancin jam’iyyar a mazaɓar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, aka jiyo shi ya dakatar da shugaban riƙo na APC ta ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, daga cikin jam’iyyar.

Sai dai daga bisani shugabancin jam’iyyar ta APC, a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, ya musanta batun dakatarwar lamarin da yace ma ana shirye-shiryen ɗaukar mataki akan waɗanda suka bayyana dakatarwar.

Continue Reading

Trending