Connect with us

Manyan Labarai

Labarai a takaice na yau Laraba 17-04-2019

Published

on

4:14pm Hukumar kula da harkokin shari’a da ladaftarwa NJC ta tabbatar da Justice Nura Sagir Umar a matsayin sabon babban jojin jihar Kano.

Kakakin kotunan Kano, Baba Jibo Ibrahim ne ya bayyana hakan cikin zantawarsa da wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il.

Rundunar ‘yansandan jihar Kano, ta fara gudanar da bincike kan wata mata mai suna Hassana Lawan mai shekaru 15 wacce ake zargin ta da zubawa mijinta mai suna Sale Abubakar mai shekara 33 shinkafar bera a cikin abinci a unguwar Bechi dake karamar hukumar Kumbotso.

A cikin wata sanarwa mai kunshe da sa hannun Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce yanzu haka mai gidan ta Sale Abubakar, ya na asibitin Murtala ana duba lafiyar sa ita kuma matar ta sa an tsare ta ana cigaba da tuhumar ta dazarar sun kammala za a gurfanar da ita a gaban kuliya.

Limamin masallacin Juma’a na Triumph Malam Lawan Abubakar, ya yi Kira ga al’umma da su rungumi turbar addu’a da ayyuka na gari, domin ta hakane za’a sami saukin yawan satar mutane da sunan kudin fansa da ake samu a wasu sassan kasar nan.

Da yake zantawa da wakilin mu Ahmad Rabi’u Ja’en, Malam Lawan ya kuma ce “matukar hukuma za ta rinka zartas da hukunci ga irin wannan mutane to babu shakka sai an samu raguwar yin garkuwa da mutane a matsayin a matsayin kudin fansa.

Hukumar Hisba a jihar Kano, ta kau want simame wata mashayar barasa dake ‘yan Katako a unguwa Uku a wani yunkuri na dakile aikata miyagun ayukan badala a sassan jihar Kano.

Yayin simamen dai jami’an hukumar Hisba sun sami nasarar kama mai siyar da barasa tare da masu shanta Wanda hukumar ta ce za ta kai su kotu domin girbar abun da suka shuka.

11:00am Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce ta fara gudanar da bincike a kan rasuwar wasu matasa biyu da jirgin kasa ya bi takan su a daren Litinin din da ta gabata sakamakon barci da su ka yi a kan titin jirgin bisa shaye-shaye da ake zargin sun yi a lokacin.

Kakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ya na mai cewa ”jami’an ‘yan sanda ne su ka dauke gawar matasan biyu zuwa Asibiti wanda likita ya tabbatar da mutuwar su”, a hannun guda kuma mun tuntubi hukumar kula da sifirin jirgin kasa dake Kano sai dai ta ce babu abin da za ta ce a kan lamarin.

Kotun Majistret mai lamba 35 karkashin mai shari’a, Sunusi Usman Atana, ta fara sauraron wata Kara da ‘yansanda su ka gurfanar da wani mutum mai suna Sulaiman Aliyu wanda ake zargin sa da laifin zamba cikin aminci da cuta wanda laifukan sun saba da sashi na 312 da na 322 kundin penal code.

Tun da fari dai wani mai suna Alh Sabi’u Muhammad ne ya shigar da Kara cewa ya baiwa Sulaiman naira miliyan daya da dubu 200 da 26 don ya yi masa safarar shinkafa buhu dari da hamsin da uku Amma Sulaiman tasarrafi da kudin sai dai kuma ya musanta zargin Wanda tini kotun ta sanya ranar 15 ga watan gobe don kawo shaidu.

Shugaban kungiyar masu sana’ar siyar da Nono a kasuwar Kofar Wambai a jihar Kano, Malam Muhammad Lawan Alaramma, ya ce “kungiyar su ta dauki gabarar tsaftace harkokin sana’ar siyar da Nono a wani mataki na zamanantar da sana’ar siyar su.

Yayin zanatawarsa ga manema labarai da ya yi, Malam Muhammad Alaramma, ya ce”tuni kungiyar ta dauki matakin yin rijista ga masu gudanar da sana’ar nono don magance bata gari a harkar.

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Continue Reading

Manyan Labarai

An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Continue Reading

Manyan Labarai

Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Published

on

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.

Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.

A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.

Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.

“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.

Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.

Continue Reading

Trending