Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Buhari zai yi jawabi a kan zazzaɓin cizon sauro a ƙasar Ruwanda

Published

on

A ranar Laraba nan ne 22-06-2023, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Kigali, babban birnin kasar Rwanda, domin halartar taron kungiyar kasashe renon Ingila karo na 26 (CHOGM).

A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar, taron wanda zai gudana tsakanin 20 zuwa 26 ga watan Yunin 2022, zai mayar da hankali ne kan ci gaba da wadata na sama da mutane biliyan biyu da suka kunshi kasashen Commonwealth.

Sanarwar ta ce, a lokacin da yake Kigali, ana sa ran Buhari zai gabatar da jawabi kan babban taron cutar zazzabin cizon sauro da rashin kula da cututtuka na wurare masu zafi, da kuma tattaunawa da wasu shugabannin da suka halarci taron.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Ƙasashen Ƙetare

Da Duminsa: Maniyaciyyar jihar Nasarawa ta rasu a kasar Saudiyya

Published

on

Maniyaciyar jihar Nasarawa mai suna, Hajiya Aisha Ahmad, ta rasu a yau Laraba sakamakon rashin lafiya a kasar Saudiyya.

Aisha Ahmed ‘yar karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa ta rasu ne bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Nasarawa Idris Al-makura ya tabbatar.

Al-Makura ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ranar Laraba a birnin Makkah na kasar Saudiyya cewa, Aisha ba ta da wani labari na rashin lafiya kafin ta tashi daga Najeriya.

Ya ce “An fara kai ta Asibitin Hukumar Alhazai ta kasa da ke Makkah, sannan aka kai ta Asibitin Sarki Abdulaziz inda ta rasu. An sanar da iyali yadda ya kamata.

Ya kuma ce, “Mun aika wa dangin ta faifan bidiyo na tsarin tabbatar da mutuwarta, zuwa ga jana’izar ta, kuma a karshe mun yi jana’izar ta,” in ji shi.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Saudiyya ta sanar da Litinin a matsayin ranar Sallar Idi ƙarama

Published

on

Kasar Saudiyya ta ce, ranar Litinin 2 ga watan Mayu a matsayin ranar Eid-el Fitr saboda ba a ga watan Shawwal ba.

Sanarwar ta ce, ba a iya ganin jinjirin watan Shawwal ba daga dakin kallo na Tamir ko kuma na jami’ar Majmaah da ke Hautat Sudair a ranar Asabar.

A cewar jaridar Saudi Gazette, hakan na nufin ranar Lahadi 1 ga watan Mayu, ita ce ranar karshe ta watan Ramadan, kuma ranar Litinin 2 ga watan Mayu, ita ce ranar farko ta Idin sallah ƙarama ta Al-Fitr.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Jack Dorsey ya samu Naira biliyan 405.3 bayan Elon Musk ya mallaki shafin Twitter

Published

on

Wanda ya kafa kuma tsohon Shugaban Kamfanin Twitter, Jack Dorsey, ya samu zunzurutun kudi har Naira Biliyan 405.3, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 977.8, bayan attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk, ya mallaki kamfanin sadarwar a ranar Litinin.

Hukumar ta Twitter ta gana da Musk da sanyin safiyar ranar Litinin, amma an tabbatar da amincewa da yarjejeniyar daga baya a ranar ta hannun hamshakin dan kasuwar.

Musk ya mallaki Twitter da sama da dala biliyan 43, bayan da ya samu dala biliyan 46.5 daga bankuna, domin samar da kudaden shiga. Shugaban Tesla da SpaceX ya na da darajar dala biliyan 268.2 har zuwa Afrilu 25, 2022.

Bayan kammala sayan, Dorsey ya samu Naira biliyan 405.3, dangane da farashin canjin kasuwa na hukuma daga yarjejeniyar, yayin da Musk ya biya dala 54.20 ga masu zuba jari da ke rike da hannun jarin Twitter.

Dorsey ya mallaki hannun jari miliyan 18.04 a shafin Twitter kafin ya fice daga mukaminsa na shugaba a watan Nuwambar bara, abin da ya sa ya zama daya daga cikin manyan masu hannun jari goma a dandalin sada zumunta kafin sayen.

Dorsey shine mutum na 356 mafi arziki a duniya. Forbes ta kiyasta darajarsa a kan dala biliyan 6.8, kuma a halin yanzu ya na shugabancin Block, wanda a da ake kira Square, wani kamfani na biyan kuɗi a Amurka. A cewar Ripple Nigeria.

Continue Reading

Trending