Labarai
Gobara ta lalata dukiya ta miliyan 34 da asarar rayuka 135 a watan Yuni – Abdullahi

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta ce, ta ceci rayuka 135 da dukiyoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 34.6 daga aukuwar gobara 42 a watan Yuni.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar,, PFS Saminu Abdullahi a Kano.
Abdullahi ya ce, mutane 24 ne suka mutu, sannan an kiyasta asarar dukiya ta Naira miliyan 13 da gobarar ta yi a lokacin.
A cewar sa, ma’aikatar ta amsa kiraye-kirayen ceto 77 da kuma kararrawar karya 17 daga mazauna jihar.
Ya danganta gobarar da rashin kula da amfani da na’urorin lantarki marasa inganci.
Ya shawarci jama’a da su rika kula, domin gujewa tashin gobara, yayin da bukukuwan Sallah ke gabatowa.
Abdullahi ya kuma bukace su da su rinka bin dokokin hanya domin gujewa hadurran mota yayin bikin.
Labarai
Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.
Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.
Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.
Labarai
Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.
SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.
Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.
Labarai
Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.
Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.
Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.
-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai2 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya2 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano