Connect with us

Kannywood

An yi jana’izzar Daraktan shirin Izzar So Nura

Published

on

Darakta a masana’antar fina-finan Kannywood, Nura Mustapha Waye ,ya rasu a safiyar ranar Lahadi.

Nura dai ya kasance daraktan fina-finai da dama ciki har da shirin nan mai dogon zango na Izzar So da a ke haskawa a shafikan Youtube.

Wakilin mu Abba Ibrahim ;Lafazi da ya halarci wajen jana’aizzar sa ya rawaito cewa, jaruman Kannywood da dama sun halarci wajen tare da yi masa addu’ar Allah ya gafarta masa.

Kannywood

Duk macen da ke da niyyar shiga harkar wasan Hausa ta dakata kada ta shigo – Alhassan Kwallai

Published

on

Shugaban ƙungiyar jarumai ta masana’antar Hausa ta Kannywood Alhassan Kwallai, ya ce duk macen da ke da niyyar shiga harkar wasan Hausa ta dakata kada ta shigo.

Alhassan Kwallai, ya bayyana hakan ne yayin zantwarsa da Dala FM Kano a yau Alhamis, ya ce kasancewar suma jaruman matan na Kannywood sun yi musu yawa, a dan haka ne yake shawartar su da su haƙura da shigowa harkar Film ɗin, domin nan gaba kaɗan ma za su rufe ƙofar shiga saboda a cikin masana’antar babu abinda babu sai rashin tsari.

A cewar sa, “Dalilin jarumai Mata yaje kotu a lokuta da dama domin a warware matsalar su, a dan haka ne ma nake shawartar su da su zauna a gidajen su ko kuma yin aure, saboda ba sai sun zo masana’antar Kannywood sannan za suyi kuɗi ba, “in ji Kwallai”.

Ya kuma ƙara da cewa dangane da dambarwar da ke faruwa a kan jarumin masana’antar Adam A Zango, ba shi da ta cewa, domin mutum yana magana ne aka abinda ya sani, shi kuwa bai san komai ba akan abinda ya shafi Zangon.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya rawaito cewa Alhassan Kwallai, ya kuma ce babu wata shawara da zai bai wa ƴan masana’antar domin kuwa mutuwa ma ta ishi kowannen su wa’azi, irin su rasuwar Jaruma Saratu Gidaɗo Daso, da ta Aminu S Bono, da sauran al’umma, kada Allah yasa ma su gyara halin nasu ga su ga Allah nan.

Continue Reading

Kannywood

Kannywood:- Moppan ta kara wa’adin yin rijista

Published

on

Hadaddiyar kungiyar masu shirya fina-finai ta Mopan tare da hadin gwiwa da hukumar tace fina finai ta Kano sun ce sun karbi koken ‘yan masana’antar Kannywood na kara wa’adin rijistar mambobin.

 

Shugaban kungiyar ta Mopan Ado Ahmad Gidan Dabino ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda yace biyo bayan koken yanzu haka ƙungiyar ta kara wa’adin zuwa 28 ga wannan wata, tare da umartar dukkanin wadanda ba suyi rijistar ba da suyi gabanin cikar wa’adin.

 

Ka zalika Ado Gidan Dabino ya kuma ce wa’adin na 28 ga wannan wata da muke ciki na zaman wa’adi na karshe da kungiyar za ta baiwa mambobin Kannywood, kuma kungiyar ta Mopan hadin gwiwa da hukumar tace fina finai ta Kano za su dauki matakin ba sani ba sabo ga dukkanin wadanda ba suyi rijistar ba har wa’adin ya cika.

 

A don haka kowa ne jarumi ya tabbatar yaje ofishin kungiyar ta Mopan dake kan titin zuwa jami’ar Bayero, kusa da ofishin Ismail Khalil Jaen domin yin rijistar.

Continue Reading

Kannywood

Daga yanzu duk kamfanin da zai dauki Film sai ya sanar da mu – Abba Al-Mustapha

Published

on

Hukumar ta ce Fina-finai ta jihar Kano, ta ce, duk kamfanin da zai yi aikin ɗaukar shirin Film, sai ya sanar da ita, sakamakon gyare-gyaren da hukumar ta zo da shi don tsaftace harkar a tsakanin al’umma.

Shugaban hukumar Abba Al-Mustafa ne ya bayyyana hakan a safiyar wannan rana ta cikin shirin barka da hantsi, na Freedom Radio Kano, ya ce ɗaukar matakin ya zama wajibi don gudun abin da ka je ya zo.

“Akwai bukatar al’umma da sauran hukumomin Gwamnatin tarayya dana jiha su ba mu hadin kai don ganin mun cimma burin mu na tsaftace harkar fina finan na Hausa; yadda za mu yi dai-dai da addini da al-adun Hausawa, “in ji Al-Mustapha”.

Continue Reading

Trending