Manyan Labarai
Zan yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Afrika ta Kudu idan na gaji Buhari – Atiku

Dan takarar shugabancin kasar nan na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, yi alkawarin muddin an zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023, zai yi aiki da ƙasar Afrika ta Kudu, domin habaka dangantakar kasashen biyu domin saura su yi koyi.
Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakwancin Jakadan Afrika ta Kudu a Najeriya, Thamsanga Dennis Mseleku a gidan sa dake Asokoro.
Sanarwar mai kunshe da sa hannun Abdulrasheed Shehu, mataimakin na musanman a kan yaɗa labarai, ya ce, tattaunawar ta su a yayin zaman ta mayar da hankali ne kan yadda za a fadada dangantakar difulomasiyya tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, domin ya zama sanadiyyar karfafa dangantaka tsakanin kasashen Afrika da nufin samar da tsarin da ake bukata na gina hadin kai da tattalin arziki a Nahiyar.
Dennis Mseleku ya ce, Najeriya na bukatar Mika mulki cikin ruwan sanyi, inda ya yi alkawarin goyon baya daga kasar sa domin Najeriya ta samu gudanar da ingantaccen zabe a 2023. Ya yabawa kasashen biyu bisa yunkurin su na sake karfafa alaka, yana mai cewa abinda kasashen biyu suka fi bukata a yanzu shi ne aiki a zahiri domin inganta tattalin arziki.
A nasa bangaren, dan takarar shugabancin kasar na PDP, ya godewa Jakadan na Afrika ta Kudu bisa ziyarar, inda ya jinjina masa bisa kokarin kyautata alaka tsakanin Najeriya da kasar sa.

Manyan Labarai
Babu ɗaga Ƙafa tsakanin mu da Ƴan Daba da masu ƙwacen Waya a Kano – Anty Snaching Phone

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Wayoyin jama’a da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye ta Anty Snaching Phone, ta gargaɗi matasan da suke addabar al’umma da faɗan Daba a cikin birnin jihar Kano, da su ƙauracewa hakan domin ba za su saurarawa dukkanin wanda ya faɗa komar su ba.
Kwamandan rundunar tsaron a jihar Kano Inuwa Salisu Sharaɗa, shi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, ya ce duk wanda suka kama da laifi musamman ma na faɗan Daba, ko ƙwacen waya ko kuma sha da dillancin kayan maye, za a ɗauki tsattsauran mataki akan sa.
“Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu ƙwacen Wayoyin jama’a, da Faɗan Daba, da kuma masu Sha da dallancin kayan Maye a jihar Kano, kuma duk wanda mu ka kama sai mun miƙa shi gurin da ya dace don ɗaukar Mataki, “in ji Inuwa Sharaɗa”.
Ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara sanya idanu wajen kula akan shige da ficen ƴaƴan su, ta yadda za su zama ababen koyi a tsakanin al’umma.
Manyan Labarai
Za’a hukunta duk ma’aikacin Shari’ar da aka samu da laifi – Babbar Jojin Kano

Babbar jojin Kano mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta jaddada cewar kwamitin ladabtarwa na hukumar Shari’a a jihar, zai hukunta duk wani ma’aikaci a tsagin Shari’a matuƙar aka same shi da laifin cin-hanci da rashawa.
Mai Shari’a Dije Aboki ta bayyana hakan ne a yayin taron ƙarawa juna sani wanda hukumar shari’ar ta gudanar ranar Talata, a ɗakin taro na Murtala Muhammad Library da ke Kano.
Taron an shirya shi ne don tunasar da sabbin ma’aikatan Shari’a, akan nauyin da ya hau kan su don mayar da hankali sosai akan batun gujewa cin-hanci da rashawa.
Babbar mai Shari’ar Dije Abdu Aboki, ta bayyana cewar akwai takaddu masu ɗauke da lambobin wayarta da aka liƙe a bangon kotuna, kuma duk wanda aka yi wa ba dai-dai ba zai iya sanar da ita ta kan lambobin kuma za a dauki mataki akan duk ma’aikacin da aka samu da laifi.
Wakilin tashar Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, a yayin taron taron ma’aikatan Shari’a da al’umma da dama ne suka samu damar halarta.
Hangen Dala
Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.
Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.
Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.
Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.
Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.
Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.
Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su