Connect with us

Labarai

Halin Tsaro: An ƙara haramta hawa Babur a jihar Katsina

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Katsina, ta tabbatar da haramcin hana hawa Babur a duka fadin jihar.

Hakan na zuwa watanni hudu, bayan da gwamnatin jihar ta dage haramcin na wucin gadi, domin sauƙaƙa wa al’umma gudanar da ibadar Azumin watan Ramadana.

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, SP Gambo Isah ya fitar, ta ce, saka dokar ya zama dole lura da yadda a baya bayannan yan ta’adda ke amfani da Baburan wurin kai hare-hare.

Ya ce, “A na jan hankalin al’umma cewa, an dabbaka dokar hana hawan Babur daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safen kowace rana.”

Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa, a jihohin da suka fi fama da hare-hare dokar za ta fara ne daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe. In ji BBC.

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending