Connect with us

Labarai

Shiyyar Arewa maso Yamma sun fi kowa yin katin zaɓen 2023 – INEC

Published

on

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa, shiyyar Arewa maso Yamma da Kudu-maso-Yamma ne ke kan gaba wajen yin rajistar masu kada kuri’a da 22,672,373 da 18,332,191.

Wani sabon rahoto da aka wallafa a shafin internet na INEC ya nuna cewa, mutane 96,303,016 ne suka yi rajista kafin a dakatar da rajistar masu zabe a ranar 31 ga watan Yuli.

A shekarar 2019, hukumar ta yi wa masu jefa kuri’a 84,004,084 rajista. Alkaluman da hukumar zabe ta INEC ta fitar a shekarar 2022 sun nuna an samu karuwar masu rajista da yawansu ya kai miliyan 12,298,932 gabanin babban zaben shekarar 2023.

Arewa-maso-Yamma, wadda ta kunshi jihohi bakwai (Jigawa, Kaduna, Katsina, Kano, Kebbi, Sokoto da Zamfara), nada masu zabe miliyan 22,672,373. Yankin Kudu-maso-Yamma da ya kunshi Legas, Oyo, Ondo, Osun da Ekiti sun bi sahun masu kada kuri’a miliyan 18,332,191.

Arewa ta tsakiya ta zo na uku da 15,680,438 da suka yi rajista, dan sama da Kudu maso Kudu da 15,299,374. Yankin Arewa-maso-Gabas na da masu jefa kuri’a 12,820,363 ya zuwa yanzu. Kudu-maso-Gabas na da mutane 11,498,277 da suka cancanci kada kuri’a.

Bayanai na INEC sun kara nuna cewa, sama da kashi 50 cikin 100 (8,854,566) na sabbin masu kada kuri’a 12,013,068 ne suka yi rajista da kansu, wasu kuma (3,444,378) sun yi rajista ta shafin hukumar.

Hakanan, sama da sabbin masu jefa ƙuri’a miliyan 12 sun ƙunshi maza 6,074,078 da mata 6,224,866.

Duk da cewa, kungiyoyin kare hakkin jama’a da jam’iyyar APC mai mulki, sun yi yunkurin tsawaita rajistar masu kada kuri’a (CVR), INEC ta ƙara wa’adin yin rajistar wanda ya ƙare a ranar 31 ga watan Yuli.

Tun da farko dai INEC ta kara tsawaita rajistar CVR daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa 31 ga watan Yuli.

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending