Connect with us

Ilimi

Alhajin Kano ɗan karamar hukumar Madobi ya rasu a Makkah

Published

on

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wani Alhaji mai suna Sani Idris Muhammed a kasar Saudiyya bayan kammala aikin Hajjin shekarar 2022.

Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin alhazai ta jiha, Alhaji Muhammed Abba Danbatta ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar.

Ya ce, Idris Muhammed wanda ya fito daga karamar hukumar Madobi, ya rasu ne a ranar Asabar bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a babban asibitin Makkah.

A cewarsa, “An yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a babban masallacin Juma’a da ke farfajiyar Masallacin Harami na Makkah”.

Abba Danbatta ya yi wa marigayin addu’a tare da miƙa ta’aziyya tare da iyalansa.

Ilimi

Mun gamsu da hana sanya kananan Siket a makarantun Anambra – MURIC

Published

on

Kungiyar kare hakkin musulmi ta (MURIC), ta jinjinawa gwamna Charles Soludo na jihar Anambra kan dokar hana ‘yan mata ‘yan makaranta sanya kananan siket a makarantun gwamnati da masu zaman kansu.

Yayin da aka koma makarantu a ranar Talatar da ta gabata, gwamnatin jihar Anambra ta ce, ta hana sanya kananan siket da dalibai mata ke yi a makarantu.

Kwamishiniyar ilimi ta jihar, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh ta ce, an haramta wa makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar.

Da take mayar da martani ga wannan ci gaban, kungiyar ta MURIC, ta bayyana cewa haramcin ya yi daidai da yunƙurin sanya hijabi da ƙungiyoyin musulmi ke yi a Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan kungiyar kare hakkin bil’adama, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce: “Gwamnan jihar Anambra, Dakta Charles Soludo ya sanar da haramta amfani da kananan siket da ‘yan matan makaranta ke yi a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a ranar Litinin, 19 ga Satumba, 2022. Mun amince da wannan karimcin. Yana da hangen nesa, mai kuzari da kishin kasa.

Continue Reading

Ilimi

Da Duminsa: Kotu ta ce lallai ASUU ta koma bakin aiki

Published

on

Kotun kolin masana’antu ta kasa ta umarci kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, da ta janye yajin aikin da ta shiga na watanni kusan bakwai da ta shiga.

Mai shari’a Polycap Hamman ta bayar da umarnin dakatar da yajin aikin ne yayin da ta ke yanke hukunci a wata takardar da gwamnatin tarayya ta shigar na neman a tilasta wa malaman jami’o’in su koma bakin aiki har sai an warware musu bukatunsu na kyautata yanayin aiki.

Kotun ta yi amfani da sashe na 18 na dokar takaddamar ciniki da kuma bukatun kasa na daliban Najeriya da su amince da bukatar gwamnatin tarayya na neman umarnin hukunta malaman.

Continue Reading

Ilimi

Zahra Buhari ta kammala karatun digiri da sakamako mai daraja ta daya

Published

on

‘Yar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhar wato Zahra Buhari, ta kammala karatun ta na digiri a fannin kimiyar gine-gine da lambar yabo mafi daraja ta daya na matakin First Class .

A wani sako da sirikar, Aisha Buhari ta wallafa a shafin ta na Facebook a ranar Talata, ta nuna hotunan Aisha Buhari da Zahra Buhari da kuma Yusuf Buhari.

Zahra Buhari ta kammala karatun digiri na farko a fannin kimiyyar gine-gine.

Ta wallafa cewa, “Ina taya Misis Zahra B Buhari murnar kammala karatunki da lambar yabo na First Class a fannin Kimiyyar Gine-gine. Ina muku fatan alheri!”

Hotunan da suka jawo ce-ce-kuce a shafukan sada zumunta daidai lokacin da a halin da ake ciki, na kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta shafe sama da watanni bakwai ta na yajin aikin masana’antu, sakamakon gazawar gwamnati wajen biyan bukatunsu.

Continue Reading

Trending