Connect with us

Labarai

Ina kan baka ta na samar da gwamnati mai cike da matasa – Atiku

Published

on

Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya jaddada aniyar sa ta samar da gwamnati mai kunshe da matasa idan ya samu dama a 2023.

A cewar mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai, Abdulrasheed Shehu, da ya raba wa manema labarai, ya ce, ɗan takarar, ya tabbatar da hakan ne yayin da matasan Jam’iyyar PDP suka gudanar da bikin ranar matasa ta duniya a ranar 12 ga Agustan 2022 a Abuja.

“Matasa ku su kansace tsayayyu wajen tallafawa PDP na kubutar da Najeriya Daga mummunan shugabanci, yajin aikin kungiyar ASUU wanda ya bar matasa zaune a gida, ilimi hakki ne ga matasa, wanda bai kamata a yi wasa da shi ba. In ji Atiku.

A jawabin sa na bude taron, shugaban matasa na Jam’iyyar ta PDP, Prince Muhammad Kadade Sulaiman, ya ce, manufar taron mai taken ‘HADIN GWIWAR GUDANAR DA SHUGABANCI TARE DA MATASA’ na cikin muradun ci gaba mai dorewa na majalisar Dinkin duniya. Inda ya bukaci a sanya matasa a cikin shugabanci tare da bukatar ɗora su a hanya da basu horo.

Ciki waɗanda suka halarci taron harda shi kansa shugaban jam’iyyar PDP Iyorchi Ayu.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending