Connect with us

Manyan Labarai

Shekarau ya tabbatar da komawa jam’iyyar PDP

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a hukumance, sakamakon cewa tsohuwar jam’iyarsa ta NNPP ba ta yi masa yadda ya ke so ba.

Shekarau ya bayyana cewa ya yi watsi da tikitin takarar Sanata na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya tarbi tsohon gwamnan zuwa PDP a gidansa na Mandubawa.

Shekarau ya bayyana cewa, ya dauki matakin ne domin dawo da adalci a Najeriya.

Sanatan mai wakiltar Kano ta tsakiya ya bada tabbacin cewa, a shirye yake ya hada magoya bayan sa a fadin kasar nan domin tabbatar da nasarar Atiku a zaben shugaban kasa na badi.

Labarai

Ranar ‘yan jaridu ta duniya: Aljanu na satar labarai daga sama – Danfodio

Published

on

Masanin harkokin aljanu a jihar Kano, Abdullahi Idris Danfodio ya ce, aljanu na satar labarai daga sama domin fada wa al’umma.

Abdullahi Idris Danfodio, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Da zarar PI ta fashe za mu yi abinda za mu taimaka wa mutane – Matashi

Published

on

Wani matashi a jihar Kano, Auwal Muhammad Musa, mai jiran fashewar PI ya ce, da zarar ta fashe za su gudanar da abubuwan da za su taimakawa al’umma.

Auwal Muhammad, ya bayyana, ya bayyana hakan ne, yayin zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa masu jiran fashewar PI na fama da matsalar damuwa – Masani

Published

on

Wani masani da ke karatun babban Digiri a jami’ar Bayero, bangaren nazarin halayyar Dan Adam a jihar Kano, Shu’aibu Lawan Matawalle, ya ce, akwai damuwa ga matasan da ke jiran fashewar PI, domin babu wanda yake samun kudi haka kawai ba tare da yayi kasuwanci ba.

Shu’aibu  Matawalle, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo, dangane da yadda matasa ke jiran fashewar PI.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Trending