Connect with us

Ilimi

Da Dumi-Dumi: Kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta kara tsawaita yajin aiki

Published

on

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU, ta tsawaita yajin aikin da take yi a yanzu haka.

Kungiyar dai ta ASUU ta tsawaita yajin aikin ne, a yayin taron majalisar zartarwa ta kasa da ta gudanar a Abuja a yau Litinin.

Wani malami a Jami’ar Calabar, UNICAL, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce: “ASUU ta sake tsawaita yajin aikin. Wannan gwamnati ta ki biyan mu, don haka ba za mu iya komawa azuzuwan ba.

Kungiyar ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun a watan Fabrairun 2022, sakamakon rashin jituwar da aka cimma da gwamnati a baya.

Ilimi

Ba Aiki Ba Biya: Mu na nan a kan bakar mu – Gwamnati

Published

on

Yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami’o’in ƙasar nan, domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin ta ce, ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba.

Ministan ilimin ƙasar Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ranar Laraba, bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin da ke Abuja.

Yayin da yake martani game da iƙirarin da shugaban ASUU ya yi na cewa gwamnati na son mayar da malaman jami’ar ma’aikatan wucin-gadi, ministan ya ce gwamnatin ba ta da wannan niyyar.

“An janye yajin aiki, kuma gwamnati ta biyasu haƙƙin iya aikin da suka yi. Ina tunani wannan shi ne matsayin gwamnati, cewa ba wanda za a biya albashin aikin da bai yi ba, sun yi aiki na kwanaki, kuma gwamnati ta biya su haƙƙinsu kwanakin da suka yi”, in ji Adamu Adamu.

Continue Reading

Ilimi

Daliban jami’ar ABU za su koma makaranta ranar 24 ga watan Oktoba

Published

on

Biyo bayan dakatar da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yi na tsawon watanni takwas, jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), ta sanar da ranar 24 ga Oktoba, 2022 a matsayin ranar da za ta ci gaba da gudanar da ayyukan ilimi.

Majalisar Dattawa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ce ta cimma matsayar.

Daraktan hulda da jama’a na Jami’ar, Auwalu Umar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, inda ya ce, an cimma matsayar ne a taron gaggawar da ta gudanar 516 biyo bayan dakatar da yajin aikin da ASUU ta yi.

Sanarwar ta ce, a zamanta na farko a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2021, a zamanta 513, majalisar ta amince da ranar, inda ta kara da cewa, saboda yajin aikin ASUU da aka tsawaita, a yanzu majalisar ta sauya ranar zuwa 24 ga watan Oktoba 2022.

Ya ce, jami’ar za ta koma ranar Litinin, 24 ga watan Oktoba, 2022, inda ta kara da cewa an shawarci dalibai da su lura da sabuwar ranar, saboda za a fara gudanar da harkokin karatu na yau da kullun.

Haka kuma ta yi kira ga daliban da su rike sabuwar kalandar jami’a ta yadda za ta yi musu jagora domin ba za a samu uzuri ga duk dalibin da ya yi biris da ranar da za a ci gaba da karatu ba.

Continue Reading

Ilimi

ICPC ta rufe sansanin masu yi wa kasa hidima NYSC na bogi

Published

on

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifukan da ke da alaka da cin hanci da rashawa (ICPC) ta rufe cibiyoyin bayar da digiri 62 a Najeriya.

Haka kuma an rufe wani sansanin horar da matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) na bogi.

Shugaban, Farfesa Bolaji Owasanoye ya bayyana hakan ne a ranar Talata a taron tattaunawa da matasa kan cin hanci da rashawa a manyan makarantun da aka gudanar a Abuja.

Owasanoye wacce wakiliyar hukumar ICPC mai kula da harkokin matasa Hannatu Mohammed ta wakilta, ta ce hukumar ta gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Shugaban ya bayyana cewa, babu wata al’umma da za ta ci gaba fiye da matakin ilimi da ingancinta.

Owasanoye ya ce hukumar ta ICPC ta kafa jami’an yaki da cin hanci da rashawa a makarantu domin dakile yaki da cin hanci da rashawa musamman manyan makarantu.

Ya ce jami’an tsaro na baiwa daliban da karfin gwiwa wajen hana cin hanci da rashawa da kuma sanya sauye-sauye a cikin abokan aikinsu.

Owasanoye ya yi nuni da cewa ICPC ta gudanar da Nazari da Bitar Tsari a tsarin Jami’o’in domin gano ayyukan da ke haifar da cin hanci da rashawa.

Binciken ya gano cin hanci,  da cin zarafi ta hanyar jima’i a wuraren.

Continue Reading

Trending