Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Ina fatan sabuwar Firaiministan Birtaniya za ta bamu hadin kai – Ukraine

Published

on

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bukaci sabon shugaban masu ra’ayin mazan jiya na Birtaniyya, Liz Truss da ta yi aiki tare da gwamnatin Ukraine don taimakawa rushe Rasha.

Zelensky, wanda ya bayyana hakan a cikin jawabinsa na yau da kullun, ya ce, ya na fatan fara haɗin gwiwa tare da Truss.

A ranar Litinin ne aka tabbatar da Truss a matsayin sabon shugaban masu ra’ayin mazan jiya na Biritaniya, wanda ya karbi ragamar mulki daga Firayim Minista Boris Johnson, daya daga cikin manyan masu goyon bayan Zelensky.

“Ina fatan fara haɗin gwiwa tare da sabuwar Firayim Ministan Burtaniya, Misis Liz Truss.

Zelensky ya ce “Mu a Ukraine mun san tana kan kyakkyawan yanayin siyasar Turai.”

Ya kara da cewa, “Kuma na yi imanin cewa, tare za mu iya yin abubuwa da yawa don kare al’ummominmu da kuma dakile duk wani yunkuri na Rasha.

“Babban abu shi ne kiyaye hadin kanmu, kuma tabbas hakan zai kasance.”

A halin da ake ciki kuma, Biritaniya ta kasance kawa ce ga Ukraine, tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Dukkanin Ukraine da Rasha sun shafe sama da watanni shida suna fafatawa.

Ya zuwa yau, an riga an sami asarar rayuka da dama a sakamakon yakin.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending