Connect with us

Labarai

Rahoto: Amfani da Turoso a gona ya na da illa a jikin Dan Adam – Malamin Jami’a

Published

on

Wani malami a tsangayar koyar da aikin gona da ke jami’ar Bayero a jihar Kano, Malam Abubakar Adamu, ya ce, amfani da Turoso a gona yana da illa a jikin Dan Adam.

Malam Abubakar Adamu, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Labarai

Ya kamata a gaggauta isar da tallafin da aka samu ga iyalan waɗanda iftila’in tankar Mai ya rutsa da su a Jigawa – Human Right

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa, da ta gaggauta isar da tallafin da gwamnatoci da kuma wasu manyan mutane suka bayar ga waɗanda iftila’in fashewar tankar dakon man fetur ya rutsa da su a garin Majia da ke ƙaramar hukumar Jigawa, al’amarin da ya shafi sama da mutane 250.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar na ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ne ya bayyana hakan yayin zanatawar sa da tashar Dala FM Kano, a ranar Lahadi 20 ga watan Oktoban 2024.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai wata babbar motar dakon man ta samu haɗari a garin Majia da ke jihar ta Jigawa, inda ta kama da wuta da hakan ya yi sanadiyyar rasuwar kusan mutane 170, yayin da fiye da mutum 100, ke kwance a Asibitoci daban-daban da suke karɓar kulawar likitoci bisa ƙonewar da sassan jikin su ya yi.

Tasi’u Idris ya kuma jajanta wa gwamnati da dukkanin al’ummar jihar Jigawa, kan faruwar al’amarin inda ya kuma miƙa ta’aziyyar su da jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa dasu.

A cewar sa, “Muna kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta gaggauta gyara wurin da motar dakon man ta yi haɗari bisa yadda titin yake haddasa haɗari tare da asarar rayuka da kuma dukiyoyin al’umma a wurin domin daƙile faruwar irin hakan a gaba, “in ji Soja”.

Rahotanni sun bayyana cewar yanzu gwamnoni da manyan ƴan kasuwa da ƴan siyasa da dama ne suka bayar da gudunmawar su domin ragewa iyalan waɗanda lamarin ya shafa wani raɗaɗi, inda zuwa yanzu aka samu sama da tallafin Naira Miliyan dubu ɗaya.

Continue Reading

Labarai

Maukibi: Mun ba za jami’an mu 1,000 domin samar da tsaro a Kano – Rundunar Anti Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen waya da kuma magance harkokin Shaye-shaye ta Anty Snaching Phone da ke jihar Kano, ta ce ta shirya samar da tsaro a yayin taron Maukibin da za a gudanar a gobe Asabar.

Kwamandan rundunar Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zanatawar sa da tashar Dala FM Kano, a ranar Juma’a.

Inuwa Sharaɗa ya kuma ce sun samu rahoton sirri kan wasu bata gari da ke shirin yin abinda bai dace ba, kuma sun shirya tsaf domin daƙile dukkan wani yunƙurin ɓata garin da ke neman tada hankalin al’umma a sassan jihar.

“Tuni gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bamu umarnin daƙile mummunar aniyar ɓata gari, kuma mun baza jami’an mu aƙalla 800 zuwa 1000, don su shiga lungu da saƙo na jihar Kano domin ganin an gudanar da Maukibin lafiya, “in ji Inuwa Sharaɗa”.

Rundunar ta kuma sha alwashin kakkaɓe dukkan ɓata garin da ke damun al’umma ta hanyar faɗan Daba da sauran miyagun ayyuka a sassan jihar Kano, tare ƙoƙari wajen ganin gwamnatin jihar ta samar wa Matasa ayyukan yi domin su dogara da kan su.

Continue Reading

Labarai

Ƴan Majalisu, Malamai, da gwamnoni ya kamata ku faɗawa Tinubu gaskiya kan halin da Talakawa suke ciki – Human Right 

Published

on

Ƙungiyar kare hakƙin ɗan adam ta Sustainable Growth Initiatives for Human Right Development, ta ce akwai buƙatar Sanatoci, da ƴan majalisar tarayya da kuma Malamai, su faɗawa shugaban ƙasa Bola Tinubu gaskiya wajen yin abinda ya dace kan tsadar rayuwar da al’umma suke ciki, biyo bayan janye tallafin man fetur, da kuma ƙarin farashin da suke samu.

Daraktan ƙungiyar a matakin ƙasa Kwamared Abubakar Musa Abdullahi, ne ya bayyanawa Dala FM hakan, a wani ɓangare na nuna takaicin sa kan yadda daga lokacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗare karagar mulki kukan al’umma ya ƙara ninkuwa, al’amarin da ke damun su.

Kwamared Abubakar Musa ya ce yadda al’ummar ƙasa suke ci gaba da fuskantar halin tsadar rayuwa, kamata ya yi ta fito da sabbin tsare-tsaren da za su taimake su, ba wai yin abinda zai ci gaba da musguna musu ba.

A cewar sa, “Daga lokacin da kuɗin man fetur ya nunka to komai ma ninkawa yake yi wanda harkokin kasuwanci, da cin Abinci ga mutane, da sauran buƙatu duk suka ɗai-ɗai ce, a don haka ya kamata Sanatoci, da Ƴan Majalisar Wakilai, da gwamnoni, da dukkanin masu ruwa da tsaki ku yi abinda ya dace domin ganin al’umma sun samu sauƙi, “in ji shi”.

Kwamared Abubakar ya ƙara da cewar ya kamata suma malamai su tashi tsaye wajen faɗawa shugabanni gaskiya, wajen ganin sun tausayawa al’umma domin samun mafita daga acikin yanayin tsadar rayuwar da suke ciki a ƙasa.

Al’ummar ƙasar nan dai sun sake shiga cikin mawuyacin hali ne tun bayan da shugaba ƙasa Bola Tinubu ya ayyana janye tallafin man fetur, jim kaɗan da rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Yanzu haka dai mafi yawan gidajen man ƴan kasuwa a sassan jihar Kano, suna sayar da kowacce litar Fetur ɗaya akan kuɗi Naira 11,00, wasu kuma 1150, zuwa 1,200, yayin da na NNPCL ke sayar da kowacce lita ɗaya 10,30, a Arewa maso Yammacin Najeriya, abin da ke damun al’umma, ki da dai a wasu ɓangarorin ƙasar yake zarta hakan.

Continue Reading

Trending