Ilimi
Za a saki sakamakon jarabawar NECO bayan tsoma bakin gwamnatin Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa, an kammala biyan kudin jarabawar hukumar shirya jarabawa ta kasa wato NECO a shekarar 2022, inda ta ce za a fitar da sakamakon a karshen wata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Magaji Dosara ya sanyawa hannu.
Kwamishinan ya shawarci iyaye da masu kula da daliban da suka zana jarabawar NECO ta 2022 da su tuntubi makarantunsu, domin samun sakamakonsu a karshen watan Satumban 2022.
Dosara, ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da su da su kara hakuri saboda ana ci gaba da tattaunawa don fitar da sakamakon jarabawar NECO na 2021.
Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an farfado da fannin ilimi a jihar ta hanyar sauye-sauye daban-daban.”

Ilimi
NECO ta saki sakamakon jarrabawar bana

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon 2023 na daliban da suka zana jarabawar tare da samun kashi 61.6 na wadanda suka samu Turanci da Lissafi.
Da yake fitar da sakamakon a ranar Talata, magatakardar hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce jimillar dalibai 1,196,985 ne suka zauna zana jarabawar.
Ya ce daga cikin jimillar dalibai da suka zauna jarabawar, 737,308 sun samu nasara da kiredit biyar zuwa sama, da suka hada da harshen Turanci da lissafi, wanda ke wakiltar kashi 61.60 cikin 100 na dalibai 1,196,985 kuma sun cancanci shiga jami’a

Addini
Abubuwan da ya kamata mu yi a lokacin da muke cikin fushi.

- Fushi daga shaidan yake
- Mu yawaita zama da Alwala da kuma ambaton Allah
- Mu guji daukar hukunci lokacin da muke cikin fushi .
A shafin sa na facebook, Falalu Dorayi yayi tsokaci kan abubuwan dake jawo fushi, da kuma hanyoyi kauce musu kamar haka
Tasirin fushi a zucivar Dan Adam na iva haifar da masifu da abubuwa marasa dadi iri iri, ciki harda kisan kai.
Duk Lokacin da Dan Adam yake cikin fushi ko wani vanayi na bacin rai,Tabbas wannan mutumin na samun bakuncin Shaidan kusa da zuciyarsa, kuma duk hukuncin da zai yi a wannan lokacin ba zai zamo mai inganci ba,ma’ana zai dauki hukunci mara dadi.
Idan muka samu kanmu a irin wannan yanayin Ma’aiki Rasulullah (SAW) Ya bamu mafita:
- Mu daura Alwala
- Mu yawaita fadin “A’udhu billahi minashaytaan-ir-rajeem”
- Idan a tsaye muke mu zauna, idan bamu daina fushin ba kuma mu kwanta.
Kada mu biyewa zuciya, mu kasance masu hakuri.
Rahoto: Koyi da halayen Annabi ne nuna tsantsar kaunar sa – Limamin Tukuntawa
Ubangiji Yana son masu hadiye fushi da yafiya lokacin da aka fusata su.
Mu duba; (Ali Imran 3:134)
Allah Yasa mu dace

Ilimi
Ba Aiki Ba Biya: Mu na nan a kan bakar mu – Gwamnati

Yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami’o’in ƙasar nan, domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin ta ce, ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba.
Ministan ilimin ƙasar Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ranar Laraba, bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin da ke Abuja.
Yayin da yake martani game da iƙirarin da shugaban ASUU ya yi na cewa gwamnati na son mayar da malaman jami’ar ma’aikatan wucin-gadi, ministan ya ce gwamnatin ba ta da wannan niyyar.
“An janye yajin aiki, kuma gwamnati ta biyasu haƙƙin iya aikin da suka yi. Ina tunani wannan shi ne matsayin gwamnati, cewa ba wanda za a biya albashin aikin da bai yi ba, sun yi aiki na kwanaki, kuma gwamnati ta biya su haƙƙinsu kwanakin da suka yi”, in ji Adamu Adamu.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano