Connect with us

Wasanni

Al-Wahda ta dauki dan wasan tsakiyar Everton

Published

on

Tsohon dan wasan tsakiya na kasar Brazil, Allan, ya bar kungiyarsa ta Everton, yayin da ya koma Al-Wahda kan kwantiragin shekaru biyu.

Allan, mai shekara 31, ya koma Everton ne a kan cinikin sama da fam miliyan 21 a shekarar 2020 daga Napoli ta Italiya.

Ya buga wasanni 52 na gasar Premier a kakar wasa biyu na farko, amma har yanzu bai buga ko da wasa daya ba a kakar 2022-23.

Frank Lampard ya sayo ‘yan wasan tsakiya da dama da suka hada da Idrissa Gueye da Amadou Onana.

Kungiyar Al Wahda ta UAE Pro League, wacce ke Abu Dhabi, ta sanar da sanya hannun a shafinta na Twitter – ko da yake Everton ba ta tabbatar da daukar matakin ba.

Tsohon kocin Swansea City da Sheffield Wednesday Carlos Carvalhal ne ke jagorantar Al Wahda, tare da tsohon dan wasan Leicester City Adrien Silva a cikin ‘yan wasan.

Wasanni

Kungiyar Al-Ittihad ta sallami mai horaswar ta Nuno.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad da ke kasar Saudiyyah ta sallami mai horaswar ta Nuno Espirito Santo, bayan kwashe watanni 16 ya na horas da ita.

Santo dan asalin kasan Portugal mai shekaru 49, kuma tsohon mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta kasar Ingila, ya fara horas da kungiyar Al-Ittihad ne a watan Yuli na shekarar 2022 bayan korar sa da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta yi.

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad dai ta bayyana cewar ta sallami Nuno Espirito Santo ne sakamakon rashin kokari da kungiyar ta ke yi karkashin jagorancin sa, Al-Ittihad dai tayi nasara ne a wasanni 6 cikin wasanni 12 da ta buga a kakar bana.

A ranar Litinin din da ta gabata ne, Kungiyar kwallon kafa ta Air Force ta kasar Iraq, ta doke Al-Ittihad da ci 2 – 0 a wasan zakarun Asian Champions league.

Continue Reading

Wasanni

Kano Pillars ta koma mataki na hudu a gasar NPFL.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta koma mataki na hudu a gasar cin kofin kwararru na Nigerian

Pillar dai ta doke Kungiyar kwallon kafa ta Bayelsa United ne, da ci uku babu ko daya a wasan mako na shida na gasar ta shekarar 2023 zuwa 2024.

A ranar lahadi 5/11/2023 ne kungiyar ta Kano Pillars za ta ziyarci Kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lagos a Jihar Lagos a wasan mako na bakwai na gasar.

Continue Reading

Wasanni

Sakamakon wasan mako na hudu na gasar NPFL

Published

on

Sakamakon wasan mako na hudu na gasar cin kofin kwararru na Najeriya na kakar 2023/2024 wato NPFL.

Tun a ranar Asabar din da ta gaba ta ne 21 Oktoba 2023, aka buga wasa daya tilo kamar haka÷

Niger Tornadoes 1 – 0 Bayelsa United

Sai dai an dage wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Doma United da Enyimba

Wasanni da aka buga a ranar Lahadi 22 Oktoba 2023 kuwa÷

Gombe United 1 – 0 Bendel Insurance

Akwa United 0 – 0 Shooting Stars

Heartland Owerri 1 – 1 Katsina United

Kano Pillars 1 – 0 Rivers United

Kwara United 1 – 1 Enugu Rangers

Lobi Stars 2 – 0 Abia Warriors

Plateau United 1 – 0 Sunshine Stars

Remo Stars 2 – 1 Sporting Lagos.

Continue Reading

Trending