Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Afrika na sawun gaba a duniya wajen yawan mutanen da ke kashe kansu – WHO

Published

on

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, Afirka ce ta fi kowace nahiya yawan mutanen da ke kashe kansu a fadin duniya.

A yanzu haka kungiyar ta kaddamar da wani gangamin yaki da ta’adar kashe kai a shafukan sada zumunta da muhawara a nahiyar, domin wayar da kan jama’a da karfafa daukar matakai.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta WHO ta fitar ta ce, kasashen Afrika 6 na cikin jerin kasashe 10 da suke da yawan masu kashe kan nasu a duniya.

A cewar BBC, Hukumar ta kuma ce likitan kwakwalwa 1 ne ke duba lafiyar mutane rabin miliyan a nahiyar ta Afrika, adadin da ya nunka shawarar masana da kashi 100 cikin 100.

Hukumar ta lura da cewa matsalar kwakwalwa ita ce babbar matsala da kashi 10 cikin 100 da ke janyo kashe kai – kuma a nahiyar Afrika kusan daukacin masu aikin jinya na kwakwalwa a birane suke.

Shugaban ofishin hukumar a Afrika, Dr. Matshidiso Moeti ya ce matsalar da ke janyo mutum ya kashe kansa matsala ce da za a iya magance ta amma kuma galibin gwamnatoci ba sa mayar da hankali a kai.

An kaddamar da gangamin na kafafen shafukan intanet ne gabanin ranar lura da lafiyar kwakwalwa ta duniya da za a gudanar a ranar 10 ga watan nan na Oktoba.

Manufar hukumar ta lafiya ta duniya ita ce yekuwarta ta kai ga mutum miliyan 10 a nahiyar Afrika.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending