Connect with us

Kasuwanci

Farashin kayan abinci sun yi tashin gauron zabi a Najeriya – NBS

Published

on

Hukumar kididdiga ta kasa, NBS, ta ce, hauhawar farashi ya yi tashin gwauron zabo da kashi 20, inda ake samun karuwar tsadar kayan abinci da makamashi da kuma ci gaba da faduwar darajar Naira.

Alkaluman hukumar sun nuna cewa, hauhawar farashin ya tashi zuwa kashi 20.77 a watan Satumba daga kashi 20.52 da yake a watan Agusta, wanda ba a taba ganin irin sa ba tun shekarar 2005.

Kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo zuwa kashi 23.4, idan aka kwatanta da kashi 23.1 da yake a watan Agusta.

Ana kuma ganin cewa matsin lamba zai iya sanya kwamitin tsare-tsare mai kula da kudi na Babban Bankin Najeriya ya kara yawan bashi da yake ciyowa a karo na hudu a jere a watan Nuwamba.

Kasuwanci

Da sana’ar siyar da Awara a bakin Titi na sayi Fili, na gina Gida, kuma nake shirin yin Aure a Kano – Mai lalurar Kafa

Published

on

Wani matashi mai lalurar Kafa da ya rungumi sana’ar siyar da Awara a gefen titin Madobi mai suna Yusif Ibrahim mazaunin Damfami dake karamar hukumar Kumbotso ya shawarci Matasa da su tashi tsaye wajen riko da kananan sana’o’i domin su dogara da kansu.

Matashin mai lalurar kafar ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakikinmu na ‘yan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, yana mai cewa riko da sana’ar na taimakawa mutum ya dogara da kansa, tare da magance wasu matsaloli da suke damunsu na yau da kullum.

“Sana’ar siyar da Awarar da nake yi da ita na sayi Fili, na gina Gida, yanzu haka kuma ina shirin yin Aure; Ina ganin budi dan haka akwai bukatar sauran matasa su nemi abin yi ko da sana’ar siyar da Awara ne, “in ji shi”.

Matashin ya kara da cewa akwai kalubale a sana’ar amma dai nasarorin sun fi yawa.

Continue Reading

Kasuwanci

Rashin tallafa mana na kawo nakasu a sana’ar mu – Masu yafin kayan lambu

Published

on

Sakatariyar kungiyar mata masu sana’ar yafin Iraruwan kayan lambu na yankin garin Ali dake karamar hukumar Garko Kubra Hassan, ta ce tallafawa masu yafin irin da abubuwan da suka sawwaka, zai taimaka musu wajen wadata kasar nan da kayan lambu ba sai an shigo da su daga kasashen ketare ba.

Kubra Hassan ta bayyana hakan ne yayin zantawarta da wakilinmu na ‘yan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, tana mai cewa yanzu haka mata sun rungumi aikin yafin iraruwan kayan lambun, amma rashin tallafa musu daga bangaren gwamnati shine babban kalubalensu wanda hakan kan kawo musu koma baya a sana’ar tasu.

“Mata ku tashi tsaye wajen rungumar kananan sana’o i domin ku dogara da kan su, tare da taimakawa kanku da ma mazajenku a gidan aure, “in ji Kubra,”

Kubra Hassan ta kuma kara da cewa, babban burinsu shine wadata kasar nan da kayan lambu mai-makon ace an dogara da na kasashen ketare.

Continue Reading

Kasuwanci

Rashin taimaka mana yana kawo mana koma baya a Kano – Manoman Tafarnuwa

Published

on

Wani manomin Tafarnuwa dake garin Kofa a karamar hukumar Bebeji mai suna Bala Abdullahi Kofa, ya ce rashin samun tallafi a sana’arsu ta noman Tafarnuwa daga gwamnati kan kawo musu koma baya.

Mallam Bala Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin zanatawarsa da wakilinmu Usaini Abdullahi Kofa a ranar Litinin, yana mai cewa matukar gwamnati ta shigo wajen tallafa musu da Taki, da samar musu da Famfon Burtsatse, babu makawa hakan zai kara bunkasa sana’ar tasu ta Noman Tafarnuwar.

Da yake nasa jawabin shima wani Manomin Tafarnuwar mai suna mallam Dalha Labaran Kofa, ya ce karin kalubalen da suke fuskanta a harkar noman Tafarnuwar shine yadda take konewa idan sun dasa ta, biyo bayan rashin wadataccen Taki da sauran matsaloli, inda suke neman daukin mahukunta.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da manoma da dama ke kara neman tallafin mahukunta, domin kara bunkasa sana’arsu ta Noma a gurare daban-daban.

Continue Reading

Trending