Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Iftila’in Ambaliya: Amurka za ta baiwa Najeriya tallafin dala miliyan 1

Published

on

Gwamnatin Amurka za ta bayar da tallafin dala miliyan 1 ga mutanen da ambaliya ta yi wa barna a Najeriya.

Tallafin da za ta bayar ta hanyar hukumarta ta raya kasashe masu tasowa (USAID), zai kasance na gaggawa.

Ruwan sama mai tsanani da ya haddasa ambaliya ya janyo illa ga kusan mutum miliyan 2.8 a fadin kasar.

Gidaje da dama sun lalace ko ma sun rushe a sanadiyyar matsalar wadda ta tashi miliyoyin mutane daga gidajensu.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurkar ya fitar a Abuja a yau Alhamis.

Amurkar ta kuma ce ta damu da yuwuwar ruwan ambaliyar da ya taru a wurare zai iya kara hadarin kamuwa da cutar amai da gudawa da sauran cutuka da ake dauka a ruwa, a jihohin Adamawa da Borno da Yobe.

A wadannan jihohin an samu barkewar cutar kwalara a watan Agusta da Satumba, kuma ta kama mutum akalla 7,750 in ji sanarwar.

A wannan shekarar da ake ciki an samu rahotannin bullar cutar ta amai da gudawa a jihohi 31 daga cikin 36 na Najeriyar.

jakadiyar Amurkar a Najeriya Mary Beth Leonard, ta ce suna cike da jimami kan wadanda ambaliyar ta shafa da suka rasa abubuwa da dama – hanyoyin rayuwarsu da gidajensu har ma da ‘yan uwansu.

Ta kara da cewa Amurka za ta ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Najeriya a wannan mawuyacin lokaci.

Sannan za ta yi aiki tare da hukumomin kasar yayin da ake sa ran samun karin ruwan sama da ambaliya a watan Nuwamba, a wasu sassan kasar saboda sauyin yanayi da rashin magudanun ruwa, da nufin samar da karin taimako idan akwai bukatar haka. In ji BBC.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending