Ƙasashen Ƙetare
A karo na biyu WhatsaApp ya katse kusan awa guda
Shafin sada zumunta na WhatsApp ya dawo aiki, bayan shafe sama da awa ɗaya da katsewa.
Da misalin karfe 8:20 na safiyar Talata, masu amfani da WhatsApp sun lura cewa ba za sa iya karba ko aika sakonni, yayin da ba.
Jama’a daga wurare daban-daban sun yi amfani da manhajojin Twitter da sauran manhajoji, domin nuna rashin jin dadinsu na katsewar shafin a wasu wurare.
Duk da haka, da karfe 9:45 na safiya, an lura cewa masu amfani sun fara karɓar saƙonni daga baya.
Sai dai mai magana da yawun shafukan sada zumunta na Meta da WhatsApp da Instagram tare da Facebook, ya magantu a kan batun cewa, tabbas suna sane da katsewar sa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.
Ƙasashen Ƙetare
Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon
Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.
Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.
Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.
Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.
Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.
Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”
Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.
Ƙasashen Ƙetare
Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar
Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.
Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.
Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.
Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.
Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.
Ƙasashen Ƙetare
An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar
Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.
Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.
Karin bayani nan tafe….
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su