Connect with us

Labarai

CBN kar ku cire rubutun larabci da na turanci a jikin sabon kudi – Adamu Garba

Published

on

Wani tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Young Progressives Party, YPP, kuma yanzu mamba a jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Adamu Garba, ya yi kira ga Babban Bankin Kasa CBN, cewa kar ya cire rubutun Larabci da Ingilish, saboda shi ne a hukumance a Najeriya.

Adamu ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da  ya ke bayyana ra’ayinsa na sake fasalin kudin Naira.

Idan za a iya tunawa, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa za a kaddamar da sabbin takardun kudi na Naira tare da wasu sauye-sauye a jikin kudin a watan Disamba na wannan shekara.

Da ya ke magana a shafinsa na Twitter, Adamu ya ba da shawarar cewa ya kamata CBN ta ci gaba da rike yarukan biyu na Ingilishi da Larabci, tare da aiwatar da canjin kudin Naira.

Daurin Boye

Mun kafa kwamiti domin rage farashin – Gwamnatin tarayya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zaiyi Duba kan hanyoyin shigo da abinci domin rage farashin sa da kaso 50.

Kwamitin dai dake karkashin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima zai yi aiki ne da wasu ministoci, domin ganin an wadatar Nigeria da abinci.

 

Yayin jawabin sa, Sanata Kashim Shettima yace hakan wani bangare NE na kara inganta tattalin arziki da shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu ke kokari.

 

Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Hangen Dala

Bamu da labarin kwankwaso zai koma APC – NNPP

Published

on

Jamiyyar NNPP a Kano tace ba ta da masaniyar labarin da ake yadawa na cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na Shirin komawa jamiyyar APC.

Shugaban jamiyyar na Kano Honorable Hashimu Suleman Dungurawa ne ya bayyana hakan ta cikin Shirin siyasa hangen dala, na tashar Dala Fm.

Yace abin da ake yadawa zance ne mara tushe balle makama, a don haka al’umma suyi watsi da wannan labari.

 

Koda dai yace su na maraba da duk wani Mataki da Sanata Kwankwason ya dauka suna tare dashi.

 

Continue Reading

Trending