Nishaɗi
Qatar 2022: Mawakin Najeriya Patoranking ya samu gurbin nishadantar da magoya baya
Fitaccen mawakin Najeriya, Patoranking, ya na jerin cikin mawakan da za su nishadantar da masoya a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a kasar Qatar.
Mawakin mai shekaru 32, a cewar bayanai a shafin intanet na hukumar kwallon kafa na duniya FIFA, zai hau matakin ne a ranar 28 ga Nuwamba.
Patoranking, wanda ainihin sunansa Patrick Nnaemeka Okorie, ya bi sawun mawaka DJ Aseel, Gims, Miami Band, Julian Marley da The Uprising, Myrath, Hassan Shakosh, da kuma Clean Bandit.
Za a iya tunawa cewa an hangi mawaki Davido da ya fito a cikin jerin mawakan da suka raira na gasar cin kofin duniya, tare da tauraruwar Amurka Trinidad Cardona da fitacciyar ‘yar Qatar Aisha.
Ana sa ran FIFA za ta fitar da wasu sunayen mawakan da za su faranta ran magoya bayanta a lokacin gasar kwallon kafa ta duniya.
Za a gudanar da gasar cin kofin duniya ta FIFA na shekarar 2022 daga ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba a wurare takwas na birane biyar na Qatar.
Kannywood
Kannywood:- Moppan ta kara wa’adin yin rijista
Hadaddiyar kungiyar masu shirya fina-finai ta Mopan tare da hadin gwiwa da hukumar tace fina finai ta Kano sun ce sun karbi koken ‘yan masana’antar Kannywood na kara wa’adin rijistar mambobin.
Shugaban kungiyar ta Mopan Ado Ahmad Gidan Dabino ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda yace biyo bayan koken yanzu haka ƙungiyar ta kara wa’adin zuwa 28 ga wannan wata, tare da umartar dukkanin wadanda ba suyi rijistar ba da suyi gabanin cikar wa’adin.
Ka zalika Ado Gidan Dabino ya kuma ce wa’adin na 28 ga wannan wata da muke ciki na zaman wa’adi na karshe da kungiyar za ta baiwa mambobin Kannywood, kuma kungiyar ta Mopan hadin gwiwa da hukumar tace fina finai ta Kano za su dauki matakin ba sani ba sabo ga dukkanin wadanda ba suyi rijistar ba har wa’adin ya cika.
A don haka kowa ne jarumi ya tabbatar yaje ofishin kungiyar ta Mopan dake kan titin zuwa jami’ar Bayero, kusa da ofishin Ismail Khalil Jaen domin yin rijistar.
Nishaɗi
Rashin jituwa tsakanin Salman Khan da Boney Kapoor zai shafi wani sabon fim
Bayan shafe shekaru ana cece-kuce, marubucin fim kuma darakta, Anees Bazmee, ya tabbatar da shirin fim dinsa na barkwanci da ya shahara a shekarar 2005 mai suna No Entry Mein Entry, tare da ainihin jarumai, Salman Khan, Anil Kapoor da Fardeen Khan cewa, watakila ya fita a watan Janairu 2023, amma da alama Salman ya zabi ficewa daga fim din ne bayan rashin jituwarsa da furodusa Boney Kapoor.
A cewar TOI, Salman ya so ya gudanar da dukkan ayyukan No Entry Mein Entry. Wannan ya zo da mamaki ga Boney wanda ya riga ya kafa tsarin samar da shi shekaru da yawa yanzu. Rahoton ya bayyana cewa bukatar Salman ta kai ga rashin jituwarsa da Boney wanda a yanzu ya yanke shawarar yin shirin No Entry ba tare da Salman Khan ba.
Idan har wannan rahoto ya zama gaskiya, to tabbas zai zama babban abin takaici ga masoyan da suka dade suna jiran ganin Salman a cikin shirin No Entry. Har ila yau, abin jira a gani shi ne ko Salman da Boney Kapoor daina nuna bambance-bambancen da ke tsakanin su kuma su kasance a wuri guda don ci gaba da tafiya kamar yadda aka tsara a baya.
Baya ga Salman, Anil da Fardeen, No Entry shima ya fito da Lara Dutta, Bipasha Basu, Esha Deol da Celina Jaitly a cikin fitattun jarumai.
Manta Sabo
Badala: Kotu ta daure mawakin Amurka R.Kelly na tsawon shekaru 30
An yanke wa mawakin R&B, R. Kelly, hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari a ranar Laraba.
Hakan ya biyo bayan hukuncin da aka yanke masa ne a shekarar da ta gabata kan laifin yin lalata. Ana zargin Kelly da yin amfani da sunansa wajen kama wadanda ya yi lalata da su cikin tarko.
Masu gabatar da kara sun bukaci alkalin da ya yanke wa dan shekaru 55 hukuncin daurin shekaru sama da 25 a gidan yari, yayin da lauyoyin da ke kare shi suka nemi a ba su 10 ko kasa da haka, suna masu cewa bukatar masu gabatar da kara ta kasance “daidai da hukuncin daurin rai da rai.
A watan Satumban da ya gabata, wata alkali ta yankewa Kelly laifi kan tuhume-tuhume tara, da suka hada da cin hanci da rashawa da kuma laifuka takwas na keta dokar, dokar safarar jima’i.
Masu gabatar da kara daga Gundumar Gabashin New York sun zargi Kelly da yin amfani da matsayinsa na shahararre da kuma “cibiyar sadarwar mutanen da ke hannun sa wajen kai hari ga ‘yan mata, maza da mata don jin dadin jima’i.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su