Connect with us

Wasanni

Har yanzu ba mu tantance cewa Mane zai je Qatar ko kuwa – Munich

Published

on

Bayern Munich ta tabbatar da cewa Sadio Mane ya samu rauni a kafarsa ta dama, amm dan wasan bai fitar da rai ba na halartar gasar cin kofin duniya na bana.

Mane ya ji rauni a wasan da Bayern ta doke Werder Bremen ranar Talata.

Daga baya Julian Nagelsmann ya bayyana cewa Mane na fama da rauni, kuma za a sake tantance shi ranar Laraba, duk da cewa rahotanni daga Faransa da Jamus sun ce tsohon dan wasan Liverpool mai shekaru 30 ba zai dawo taka leda ba a lokacin da zai buga wa Senegal a Qatar.

A ranar Laraba, Bayern ta tabbatar da yanayin raunin da Mane ya samu, inda matsalar ta ci gaba da kasancewa a saman kafarsa na dama.

Bayern ta ce: “Mane ya ji rauni a kafarsa na dama, ba zai buga wasan mu da Schalke ba.”

“Za a ci gaba da yin gwaje-gwaje nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, FC Bayern za ta tuntubi bangaren likitocin hukumar kwallon kafa ta Senegal.”

A ranar Juma’a ne dai kasashen da suka lashe gasar cin kofin Afrika suka bayyana sunayen ‘yan wasan nasu, kuma abin jira a gani shi ne ko Mane zai shiga cikin su, duba da irin muhimmancin da yake da shi ga damar da Senegal ta samu na tsallakewa daga rukunin A, da ya kunshi Netherlands da Ecuador da Qatar mai masaukin baki.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending