Connect with us

Wasanni

Manchester City za ta gamu da Liverpool a Carabao

Published

on

Liverpool mai rike da kofin Carabao, za ta kara da takwararta ta Manchester City a wasan zagaye na hudu na gasar.

Liverpool ta tsallake zuwa zagaye na hudu a bugun fanareti a hannun Derby County ranar Laraba, yayin da City ta riga ta yi waje da abokan hamayyarta a Chelsea sakamakon nasarar da ta ci 2-0.

Idan City za ta iya doke Liverpool, za ta sake zawarcin damar zuwa gaba, bayan da ta lashe kofin EFL sau shida a cikin shekaru tara da suka wuce.

Hudu daga cikin nasarorin da aka samu sun samu ne tun bayan da Pep Guardiola ya karbi ragamar horar da ‘yan wasan kuma guda daya za su kai ga samun nasara a tarihin Liverpool na cin kofin EFL guda tara.

Manchester United ta samu tikitin shiga gasar, bayan ta doke Aston Villa da ci 4-2 a ranar Alhamis. Kuma za su kasance da kwarin gwiwar samun hanyar da za ta kai ga zagaye na gaba bayan sun yi kunnen doki da Burnley a gasar Championship, wanda Vincent Kompany ke kula da kungiyar.

Newcastle da Bournemouth za su fafata a gasar Premier, yayin da Blackburn ke jiran Nottingham Forest.

Kungiyar Gillingham ta League Two, wacce ke matsayi mafi karanci da ta rage a gasar, za ta kara da abokan hamayyar Premier a Wolves.

Har ila yau, Lincoln na League One yana da babbar rana a gabansu yayin da za su je Southampton, yayin da wata ƙungiya ta uku – MK Dons – za ta fafata da Leicester.

Charlton, daya tilo da ke Landan, ta na maraba da Brighton zuwa The Valley, bayan Seagulls ta kawar da Arsenal.

Za a buga dukkan wasannin ne a cikin makon da zai fara ranar 19 ga Disamba.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending