Connect with us

Ilimi

Ba Aiki Ba Biya: Mu na nan a kan bakar mu – Gwamnati

Published

on

Yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami’o’in ƙasar nan, domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin ta ce, ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba.

Ministan ilimin ƙasar Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ranar Laraba, bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin da ke Abuja.

Yayin da yake martani game da iƙirarin da shugaban ASUU ya yi na cewa gwamnati na son mayar da malaman jami’ar ma’aikatan wucin-gadi, ministan ya ce gwamnatin ba ta da wannan niyyar.

“An janye yajin aiki, kuma gwamnati ta biyasu haƙƙin iya aikin da suka yi. Ina tunani wannan shi ne matsayin gwamnati, cewa ba wanda za a biya albashin aikin da bai yi ba, sun yi aiki na kwanaki, kuma gwamnati ta biya su haƙƙinsu kwanakin da suka yi”, in ji Adamu Adamu.

Ilimi

Za’a daga likafar BMC zuwa Diploma – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin Kano tace nan bada jimawa ba za’a daga likafar makarantar koyon aikin jarida a matakin farko wato BMC ta Goron Dutse zuwa tsarin Diploma.

Mataimakin gwamnan Kano Kwamred Aminu Abdussalam ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake jawabi a wurin taron da kungiyar tsaffin daliban makarantar suka shirya.

Kwamred Aminu Abdussalam ya kuma ce nan bada jimawa ba makarantar za’a daga matsayin karatun daga Certificate zuwa Diploma, kamar yadda makarantar ta bukata.

Kazalika yace gwamnatin Kano za ta cigaba da lura da dukkanin kayan koyo da koyarwa har ma da ababen hawa na hukumar ilimin manya ta Kano, wato Agency for mass Education wadda a cikin ta ake karatun na jarida.

Taron dai wanda shi ne karo na farko da gamayyar kungiyar daliban ta shirya tun bayan kafuwar makarantar shekaru 38 da ta gabata, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka haɗar da Kwamishinan ilimi na Kano da Kwamishinan yada labarai da kwamishiniyar mata da mai baiwa gqamna shawara kan harkokin yada labarai.

Kazalika taron ya samu halartar Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da tsaffin malaman makarantar da kuma shugabannin kafafen yada labarai na Kano.

A yayin taron dai shugaban kungiyar taaffin daliban Ismaila Ammai me Zare ya kaddamar da wani tsari na tallafawa makarantar da abin zama mai taken ( ka dawo da kujerar ka ).

Continue Reading

Ilimi

Ma’aikatar Ilimi ta jihar kano ta sanar da ranar komawar Dalibai makaranta

Published

on

Ma’aikatar Ilimi ta jihar kano ta sanar da ranar komawa makaranta, domin fara daukar karatun zango na biyu, ga daliban makarantun kwana dama na jeka ka dawo.

Ma’aikatar Ilimin ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, inda ta ce za’a koma makarantar ne a ranar litinin 8 ga watan janairun sabuwar shekarar 2024, da ake ciki a yanzu.

A cewar sanarwar, daliban makarantun kwana zasu koma ne a gobe lahadi 7 ga watan Janairu domin fara daukar darasin, inda kuma ga daliban makarantun firamare dama na sakandiren za su koma a ranar Litinin.

Haka kuma sanarwar Daraktan ta kuma bukaci iyaye dama wakilan daliban suyi biyayya ga dukkan ka’idojin komawa makarantar, inda ya ce zasu dauki mataki ga daliban da suka bijirewa umarnin komawar.

Sanarwar ta kuma yabawa gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusif, a bisa yadda ta gyara motocin kai yara makaranta, domin daliban suji dadin zuwa koyon karatun cikin sauki.

Daga bisani dai sanarwar ta ambato kwamishinan ilimi na jihar kano Alhaji Umar Haruna Doguwa, na fatan malamai dama daliban za suyi karatun zango na biyun cikin nasara, tare da jaddada sanya idanu akan yadda malaman makarantun jihar suke gudanar da ayyukan su bisa tsari.

Continue Reading

Ilimi

Gwamnatin Kano ta sanar da ranar komawa makaranta

Published

on

Ma’aikatar Ilimi ta jihar kano ta sanar da ranar komawa makaranta, domin fara daukar karatun zango na biyu, ga daliban makarantun kwana dama na jeka ka dawo.

Ma’aikatar Ilimin ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, inda tace za’a koma makarantar a ranar litinin 8 ga watan janairu sabuwar shekarar da muke ciki ta 2024.

Sanarwar ta kara da cewa daliban makarantun kwana zasu koma ne a gobe lahadi 7 ga watan domin fara daukar darasin, ga daliban makarantun firamare dama na sakandire.

Sanarwar Daraktan ta kuma bukaci iyaye dama wakilan daliban suyi biyayya ga dukkan ka’idojin komawa makarantar,inda yace zasu dauki mataki ga daliban da suka bijirewa umarnin.

Haka kuma sanarwar ta yabawa gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Injijiya Abba Kabir Yusif,a bisa yadda ta gyara motocin kai yara makaranta,domin daliban suji dadin zuwa koyon karatun.

 

A karshe sanarwar ta ambato kwamishinan ilimi na jihar kano Alhaji Umar Haruna Doguwa, na fatan malamai dama daliban zasuyi karatun zango na biyun cikin nasara,tare da jaddada sanya idanu akan yadda malaman makarantun jihar suke gudanar da ayyukan su.

Continue Reading

Trending