Connect with us

Wasanni

‘Yar wasan Najeriya Oparanozie ta lashe gasar kasar Sin

Published

on

‘Yar wasan gaba ta Super Falcons, Desire Oparanozie, ta lashe kofin gasar mata ta kasar Sin tare da Wuhan Jiangda ranar Asabar.

Bangaren Liu Lin ya lashe kambun karo na uku a jere.

Wuhan Jiangda ita ce ta daya a kan teburi da maki 45 a wasanni 18.

Sun yi nasara a wasanni 15, inda suka sha kashi uku kacal a duk tsawon wasannin da su ka yi a gasar.

Jiangsu Suning ta zo ta biyu da maki 39 daga yawan wasannin.

Oparanozie ta na da alaƙa da Wuhan a wannan shekara daga ƙungiyar Faransa, Dijon.

Temwa Chamwinga ta Malawi ita ce ‘yar Afirka a cikin tawagarsu ta biyu.

Wasanni

Kano Pillars ta sayi Salisu Abdullahi

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Capital City da take a babban birnin tarayya Abuja wato Salisu Abdullahi

Salisu ya rattaba kwantaragin shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru tare da yan wasan kungiyar, dan ganin kungiyar ta samu nasarori a gasar da zata buga ta cin kofin kwararru na Nigeria ta shekarar 2023 zuwa 2024.

Continue Reading

Wasanni

Chelsea ta sayi Lavia daga Southampton

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Southampton wato Romeo Lavia a kan kudi €58m.

Romeo Lavia, dan asalin kasar Belgium mai shekaru 19, ya rattaba kwantaragin shekaru bakwai da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Kafin komawar dan wasa Lavia kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Southampton wasanni 34.

“Ina farin cikin komawa ta kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kuma komawar ta zo min kamar a mafarki, domin Chelsea kungiya ce da take da tarihi kuma kowanne dan wasa zai so ace yana buga wasa a Chelsea, kuma zan hada kai da abokan wasana dan ganin mun kai kungiyar mu ga babban mataki” a cewar Lavia.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta dauki sabbin yan wasa

Published

on

A yunkurinta na tunkarar sabuwar kakar wasan gasar Firimiyar Nigeria wato NPFL ta shekarar 2023 zuwa 2024, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sayi sabbin yan wasa guda uku domin yin garan bawul ga kungiyar.

‘Yan wasan dai sun hadar da Ibrahim Mustafah Yuga da Abubakar Ibrahim Babawo wayanda suka tawo daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Plateau United dake jihar Jos, sai kuma Abubakar Aliyu daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourists dake jihar Bauchi, sanarwar dai ta fito ta hannun mai magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa.

Continue Reading

Trending