Connect with us

Wasanni

FA ta ci tarar Ronaldo Fam dubu 50 da dakatar da shi a gasar Firimiya

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila FA, ta ci tarar Kyaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo tarar fan 50,000 tare da dakatar da shi wasanni biyu.

Bayan da Manchester United ta sha kashi a hannun Everton a filin wasa na Goodison Park a kakar wasan da ta wuce, Ronaldo ya bayyana ya mari hannun wani magoyin bayan Everton a lokacin da ya kutsa cikin ‘yan kallo, inda ya lalata wayar magoyin bayan.

Yanzu dai hukumar ta FA ta kammala binciken ta kuma ta ci tarar dan wasan mai shekaru 37 da haihuwa da kuma dakatar da shi, in ji jaridar The Mirror.

Ronaldo ya yarda cewa ba daidai ba ne bayan wasan da Manchester United ta buga da Everton a ranar Asabar, 9 ga Afrilu, 2022, bai dace ba.

Wata hukumar da ke da zaman kanta ta gano cewa, Ronaldon ya aikata rashin adalci da tashin hankali a yayin sauraren karar da ya biyo baya kuma ya sanya wa dan wasan takunkumin.

Wannan na zuwa ne kasa da kwana guda bayan Man United ta soke kwantiragin Ronaldo.

A halin yanzu Ronaldo ya na tare da tawagar ‘yan wasan kasar Portugal a Qatar yayin da suke shirin karawa da Black Stars na Ghana a gasar cin kofin duniya da za su kara a ranar Alhamis.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending