Manyan Labarai
Faransa ta kai wasan zagaye na biyu a Qatar bayan ta doke Denmark

Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa kwallo biyu a lokacin da zakarun gasar suka kafa wata ta doke Denmark da ta zama ta farko a gasar cin kofin duniya da ta tafi wasan zagaye na biyu a gasar.
Dan wasan mai shekaru 23, dan kasar Faransa mafi karancin shekaru a gasar, ya sake satar wasan da bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Tun da farko Mbappe ya buga daga yadi 12 sannan ya tilastawa Kasper Schmeichel kwallon ta shiga raga.
Sai dai dan wasan na Paris St-Germain ya tsallake rijiya da baya bayan an wuce sa’a daya, inda suka yi musabaha mai kyau daya da biyu da Theo Hernandez kafin ya zura kwallo a raga.
Dan wasan Denmark Andreas Christensen ya farke kwallo ta farko bayan minti bakwai kacal bayan da Faransa ta farke kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Manyan Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.
Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”

Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.
Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.

Labarai
Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.
Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano