Connect with us

Wasanni

Mai horas da Brazil ya ajiye aikinsa bayan an yi waje da Brazil a Qatar

Published

on

Mai horas da tawagar ƙwallon ƙafa ta Brazil, Tite, ya ajiye aikinsa bayan Croatia ta fitar da su daga Gasar Kofin Duniya a bugun finareti a wasan kwata fayinal da suka buga ranar Juma’a.

Kocin mai shekara 61, ya jagoranci Brazil tun daga 2016 kuma ya taɓa faɗa cewa zai bar aikin bayan gasar ta 2022 da ake yi a Qatar.

“Abin da ciwo amma na tafi ke nan. Ƙarshen lamarin ke nan a wajena,” kamar yadda ya faɗa wa ‘yan jarida bayan wasan da aka buga a filin wasa na Education City Stadium.

“Da ma na faɗi haka shekara ɗaya da ta wuce. Ban zo nan don na ci kofi ba kuma na ce zan ci gaba da aiki, waɗanda suka san ni sun san haka.”

Croatia ta doke Brazil 4-2 a bugun finareti bayan wasan ya tashi 1-1, inda ɗan wasa Neymar ya kamo Pele a yawan ci wa Brazil ƙwallaye da 75 kowannensu.

Akwai yiwuwar shi ma ɗan wasa Neymar ya jingine takalmansa saboda ya ce “babu tabbas ko zan sake buga wa Brazil wasa”. In ji BBC.

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Trending