Manyan Labarai
Shugaban kasa zai halarci yakin neman zaben Aisha Binani a Jihar Adamawa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihohi goma domin yakin neman zabe
- Buhari zai je jihar Adamawa domin yakin neman zaben Aisha Binani
- An tabbatar da tsaro a jihar Adamawa
Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta girke jami’anta domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya yayin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Adamawa SP Sulaiman Nguroje ne ya bayyana hakan da yammmacin ranar asabar 7 ga watan janairun nan da muke ciki a babban birnin jihar Yola.
SP Suleiman ya kara da cewa suna sa ran jami’an tsaron na su zasu sa ido wajen tabbatar da komai ya tafi daidai kamar yadda ya kamata.
Kakakin yace” kwamishinan yan sandan jihar yana aiki kafada da kafada da al’ummar jihar domin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa”
Sulaiman yace kwamishinan yan sandan ya umarci da a rage yawan zirga-zirgan ababen hawa, musamman ma a kusa da inda za’a gabatar da taron.
Jam’iyyar APC ba ta da dan takarar gwamna a Adamawa bayan fatali da Aisha – Kotu
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Shugaba Buhari zai isa birnin ne dan kaddamar da yakin neman zaben yar takarar gwamnan jihar wato Sanata Aisha Binani.

Manyan Labarai
DSS sun kama Emefele bayan dakatar dashi daga Gwamnan banki

Rahotanni na cewa jami’an tsaro na farin kaya DSS sunyi awon gaba da Godwin Emefele, sa’a guda bayan Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya dakatar dashi daga Gwamnan babban banki.
Tun abaya dai an zargi Emefele da hannu wajen gurgunta tattalin arzikin kasa, baya ga zargin sa, da hannu wajen tabarbarewar tsaro.

Manyan Labarai
Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.
Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.
” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.
Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.
Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Manyan Labarai
Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.
Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano