Connect with us

Manyan Labarai

Wani Matashi ya kashe matar Baban shi da ‘yar ta a kano.

Published

on

Rundunar yan sandan jihar kano ta kama wani matashi dan kimanin shekaru 20 mai suna Gaddafi Sagir da laifin kashe Kishiyar Mahaifiyarsa da kuma yar’ ta.

Lamarin ya faru ne a daren Asabar 7 ga watan janairu 2023 da misalin karfe 11 na dare,a Rijiyar Zaki layin Dorawar Yan’kifi dake jihar kano.

A cewar yaron Gaddafi ya aikata hakanne saboda marigayiyar;Malama Rabi,ita tayi sanadiyyar Rabuwar Mahaifinsa Malam Sagir Mai magani da kuma mahaifiyarsa.

Ita kuma yarinyar yace ya kashe ta ne saboda ta ga lokacin da yake kashe marigayiyar;wato mahaifiyarta.

Kotu ta yanke wa wata matashiya hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

Kakakin Rundunar yan sandan jihar kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin,inda kuma yace suna nan suna kara bincike a kai.

Manyan Labarai

DSS sun kama Emefele bayan dakatar dashi daga Gwamnan banki

Published

on

Rahotanni na cewa jami’an tsaro na farin kaya DSS sunyi awon gaba da Godwin Emefele, sa’a guda bayan Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya dakatar dashi daga Gwamnan babban banki.

Tun abaya dai an zargi Emefele da hannu wajen gurgunta tattalin arzikin kasa, baya ga zargin sa, da hannu wajen tabarbarewar tsaro.

Continue Reading

Manyan Labarai

Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Published

on

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.

Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.

” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.

Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.

Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

Continue Reading

Trending