Wasanni
Kungiyar Southampton ta sayi Alcaraz

Kungiyar kwallon kafa ta Southampton da ke kasar Ingila ta sanar da sayan dan wasa Carlos Alcaraz mai shekaru 20 daga kungiyar kwallon kafa ta Racing Club da ke kasar Argentina.
Alcaraz mai buga wasa a tsakiya ya rattaba kwantaragin shekaru biyu da rabi da kungiyar ta Southampton “Ina matukar farin cikin kasancewa ta cikin wannan kungiya, duk da nasan haka zai zama sabon kalubale a gare ni da aiki na inji Alcaraz “
Dan wasa Carlos Alcaraz zai iya buga wasan sa na farko a gasar firimiyar kasar ta Ingila, inda Southampton din zata kara da kungiyar kwallon kafa ta Everton a ranar 14 ga watan janairun nan da muke ciki, idan sun gabatar da cikakkun takardun sa da ake bukata a ranar juma’a mai kamawa.

Wasanni
Dembele ya tallafawa Barcelona ta kai wasan kusa da na karshe

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ousmane Dembele ne, ya zurawa Barcelona kwallo daya tilo a wasan kusa da na karshe da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad, a gasar Copa Del Rey da ke gudana a kasar ta Spain, wanda hakan ne yabawa Barcelona damar zuwa wasan kusa da na karshe a gasar.
Kawo yanzu, dan wasa Ousmane Dembele ya zurawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kwallaye bakwai a kakar wasannin nan da muke ciki.

Wasanni
Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki aron Danjuma daga Villarreal

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta sanar da daukan aron dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Villarreal dan asalin kasar Netherlands wato Arnaut Danjuma mai shekaru 25 har zuwa karshen kakar nan da muke ciki.
Tun bayan da aka bude kasauwar saye da sayarwa na ‘yan wasanni a watan janairun nan da muke ciki, Arnaut Danjuma, shine dan wasa na farko da Tottenham Hotspur din ta dauka.
Tottenham Hotspur ta na mataki na biyar a teburin gasar firimiyar kasar Ingila ta shekarar 2022 zuwa 2023 da muke ciki.

Wasanni
Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kori Lampard

Tsohon da wasan kasar Ingila mai shekaru 44 Lampard ya karbi aikin horas da kungiyar kwallon kafa ta Everton a watan janairun shekarar 2022 da ta gaba ta, bayan sallamar mai horas da ita na wancan lokacin Rafael Benitez.
Everton dai ta yi rashin nasara a wasanni tara cikin wasanni 12 da ta buga a gasar Firimiyar kasar Ingila ta shekarar 2022 zuwa 2023 da muke ciki.
A ranar Asabar din da ta gabata dai kungiyar kwallon kafa ta Everton ta yi rashin nasara a karawar da ta yi da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United, wanda hakan yasa ta ke mataki na 19 da maki 15 a teburin gasar ta bana.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya8 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano