Manyan Labarai
Na sauke nauyin da ‘yan Nigeria suka dora min – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya mulki Najeriya da iyakar ƙokarinsa, inda ya ce bai ba wa ‘yan ƙasar kunya ba.
Shugaban wanda ya je jihar Bauchi a cigaba da ƴaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na shugaban ƙasa da kuma na gwamna, ya bayyana hakane lokacin da ya kai ziyara gidan Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu.
Buhari ya ce dubban mutane da suke fitowa su tarbe shi a duk inda ya je hakan na nuna ƙarara irin soyayyar da ake masa.
“Ina so na faɗa cewa tsakanin 2003 zuwa 2011, na kai ziyara dukkanin ƙananan hukumomin Najeriya, sannan a 2019, lokacin da nake neman sake komawa kan mulki ƙaro na biyu, na ziyarci dukkanin jihohi a faɗin ƙasar, mutanen da naga sun fito tarba ta, abu ne da ba zan iya misaltawa ba saboda dandazonsu, a lokacin na yi alkawarin mulkar Najeriya da ‘yan Najeriya da iyaƙar ƙokarina kuma zuwa yanzu na san na yi ƙokari,” in ji shugaban.
Tun da farko a jawabinsa, Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman, ya ce abu mai kyau ne idan shugabannin siyasa suka nuna girmamawa ga Sarakuna da kuma masarautu ta hanyar kai musu ziyara.
Ya godewa shugaba Buhari kan irin ci gaban da gwamnatinsa ta kawo a Bauchi, inda ya ce aikin haƙo man fetur na Kolmani, wani bu ne da ‘yan jihar da ma arewa maso gabas ba za su manta ba.

Manyan Labarai
Shekaru 63 na Nigeria:- Jawabin Gwamnan Kano

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci shugabanni da saura al’umma da suyi koyi da tsaffin shugabannin da suka gabata wajen kawowa ƙasar nan ci gaba da zaman lafiya musamman a irin wannan lokaci.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yau yayin da yake jawabi kan cikar ƙasar nan shekara 63 da samun kyancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.
Gwamna Abba ya kuma ce la’akari da yadda ake tunawa da tsaffin shugabanni wajen ciyar da ƙasar nan gaba ya kamata su shugabannin yanzu suyi koyi da su.
Ka zalika ya ƙara da cewa ya kamata shugaban ni su tabbata sun yiwa al’umma abin da suke buƙata domin tabbatar adalci.
Gwamnatin tace zata ci gaba da gudanar da aikin ta kamar yadda ta tsara domin ciyar da Kano gaba.

Hangen Dala
Hukuncin Kaduna :- PDP za ta daukaka kara

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ta tabbatar da zaben Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC, inda ta ce za ta garzaya kotun daukaka kara.
Alberah Catoh, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a a Kaduna.
Catoh ya ce, wani nazari da lauyan PDP ya yi ya nuna cewa hukuncin bai cika wasu ka’idoji na tabbatar adalci ba.
Martanin ya zo ne sa’o’i bayan kotun da ke zamanta a Kaduna ta amince da nasarar zaben Sani.
Ya kara da cewa hukuncin bai dace da wasu dokoki da ka’idojin zabe ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda haka jam’iyyar ta umurci lauyoyinta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara da ke Abuja a cikin wa’adin da doka ta kayyade.”
Catoh ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar PDP a fadin jihar da su kwantar da hankalinsu tare da nuna kwarin gwiwarsu kan lamarin.

Hangen Dala
Abba ya biyawa Daliban Kano kudin makaranta

Abba Kabir ya biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero
Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero, waɗanda ba su samu damar biya ba, kimanin Naira Miliyan ɗari bakwai.
Sakataren hukumar bayar da tallafin ilimi ta jihar Kano, Hon. Kabir Getso Haruna ne, ya bayyana hakan a ranar Talata.
Yana mai cewa, “Yanzu haka Gwamnatin Kano, ta biya wa ɗalibai ƴan asalin jihar, dubu bakwai kuɗin makarantar”.
Ya kuma ce, “Daga yau Talata, dukkan ɗaliban, su tafi Jami’ar Bayero, tsangayoyin su, domin ƙarasa rijista na shekarar 2023, su ci gaba da karatu”. Inji Hon. Kabir Getso.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano