Connect with us

Wasanni

Silva ya tsawaita kwantaraginsa da Chelsea

Published

on

Thiago Silva wanda ke buga wasa a baya, ya sake tsawaita kwantaraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na tsawon shekara daya, inda kwantaragin zai kare a shekarar 2024.

Silva mai shekaru 38, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga PSG ta kasar Faransa a shekarar 2020, kawo yanzu ya bugawa Chelsea wasanni 106.

Thiago Silva wanda dan asalin kasar Brazil ne, ya tallafawa Chelsea ta samu nasarori da dama wanda daga ciki harda nasarar lashe kofin zakarun nahiyar Turai.

Wasanni

Tsohon mai horas da Super Falcons Mabo ya rasu.

Published

on

Tsohon mai horas da tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta mata ta kasa, Super Falcons, Ismaila Mabo, ya rasu ya na da shekaru 80 a duniya.

Dan uwansa Salisu Nakande Mamuwa ne ya bayyana rasuwar ta sa a shafin sa na sada zumunta a safiyar yau Litinin.

Karanta wannan labarin: http://flying eagles

Kafin rasuwarsa dai Ismaila Mabo ya jagoranci Super Falcons a gasar cin kofin duniya na mata, inda ya jagorance su zuwa wasan dab da na kusa da na karshe a shekarar 1999, ya kuma jagorance su zuwa gasar wasannin Olympics a shekarar 2000 da kuma 2004.

Continue Reading

Wasanni

Za a iya Conte aikin gaggawa a mafutsara – Tottenham

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, ta baiwa mai horas da kungiyar, Antonio Conte, hutu yayin da a yau ake shirin yi masa aikin tiyatar gaggawa a mafutsararsa.

Kungiyar ta Tottenham ta tabbatar da hakan a wata sanarwar da ta wallafa a shafin ta na internet.

Conte ya kamu da rashin lafiya a farkon wannan makon, kuma ya koka da matsanancin ciwon ciki.

An gano tsohon manajan na Chelsea ya na da cutar cholecystitis, yanayin da ke haifar da kumburi da ja na mafutsara.

Labarai mai alaka: Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki aron Danjuma daga Villarreal

Sanarwar ta Tottenham ta ce “A kwanan nan Antonio Conte ya yi rashin lafiya tare da matsanancin ciwon ciki.”

“Bayan an gano cutar cholecystitis, yau za a yi masa tiyata a mafitsara a yau, kuma zai dawo bayan wani lokaci idan ya samu murmurewa. Kowa a kungiyar ya na yi masa fatan alheri.” Inji Tottenham.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar Bournemouth ta sayi dan wasan kasar Ghana Semenyo

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth da ke kasar Ingila, ta sanar da sayan dan wasan gaban kasar Ghana da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Bristol City wato Antoine Semenyo akan kudi yuro miliyan tara.

Semenyo mai shekaru 23, ya rattaba kwantaragin shekaru hudu da rabi da kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth, tare da yarjejeniyar kara kwantaraginsa da kungiyar a nan gaba.

Antoine Semenyo na daya daga cikin ‘yan wasan da kasar Ghana ta je da su wasan gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 da kasar Qatar ta karbi bakwanci, ya kuma zurawa kungiyar kwallon kafa ta Bristol City kwallaye 21 a wasanni 125 da ya buga mata.

Yanzu haka dai Antoine Semenyo shine dan wasa na uku da Bournemouth ta saya a watan janairun nan da muke ciki, da suka hadar da mai tsaron raga Darren Randolph da Dango Ouattara sai kuma Antoine Semenyo.

Continue Reading

Trending