Connect with us

Wasanni

Za a iya Conte aikin gaggawa a mafutsara – Tottenham

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, ta baiwa mai horas da kungiyar, Antonio Conte, hutu yayin da a yau ake shirin yi masa aikin tiyatar gaggawa a mafutsararsa.

Kungiyar ta Tottenham ta tabbatar da hakan a wata sanarwar da ta wallafa a shafin ta na internet.

Conte ya kamu da rashin lafiya a farkon wannan makon, kuma ya koka da matsanancin ciwon ciki.

An gano tsohon manajan na Chelsea ya na da cutar cholecystitis, yanayin da ke haifar da kumburi da ja na mafutsara.

Labarai mai alaka: Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki aron Danjuma daga Villarreal

Sanarwar ta Tottenham ta ce “A kwanan nan Antonio Conte ya yi rashin lafiya tare da matsanancin ciwon ciki.”

“Bayan an gano cutar cholecystitis, yau za a yi masa tiyata a mafitsara a yau, kuma zai dawo bayan wani lokaci idan ya samu murmurewa. Kowa a kungiyar ya na yi masa fatan alheri.” Inji Tottenham.

Wasanni

Kano Pillars ta sayi Salisu Abdullahi

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Capital City da take a babban birnin tarayya Abuja wato Salisu Abdullahi

Salisu ya rattaba kwantaragin shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru tare da yan wasan kungiyar, dan ganin kungiyar ta samu nasarori a gasar da zata buga ta cin kofin kwararru na Nigeria ta shekarar 2023 zuwa 2024.

Continue Reading

Wasanni

Chelsea ta sayi Lavia daga Southampton

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Southampton wato Romeo Lavia a kan kudi €58m.

Romeo Lavia, dan asalin kasar Belgium mai shekaru 19, ya rattaba kwantaragin shekaru bakwai da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Kafin komawar dan wasa Lavia kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Southampton wasanni 34.

“Ina farin cikin komawa ta kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kuma komawar ta zo min kamar a mafarki, domin Chelsea kungiya ce da take da tarihi kuma kowanne dan wasa zai so ace yana buga wasa a Chelsea, kuma zan hada kai da abokan wasana dan ganin mun kai kungiyar mu ga babban mataki” a cewar Lavia.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta dauki sabbin yan wasa

Published

on

A yunkurinta na tunkarar sabuwar kakar wasan gasar Firimiyar Nigeria wato NPFL ta shekarar 2023 zuwa 2024, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sayi sabbin yan wasa guda uku domin yin garan bawul ga kungiyar.

‘Yan wasan dai sun hadar da Ibrahim Mustafah Yuga da Abubakar Ibrahim Babawo wayanda suka tawo daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Plateau United dake jihar Jos, sai kuma Abubakar Aliyu daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourists dake jihar Bauchi, sanarwar dai ta fito ta hannun mai magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa.

Continue Reading

Trending