Connect with us

Manyan Labarai

Matakin INEC Kan shugaban ta na jihar Adamawa

Published

on

Hukumar zaɓe ta kasa INEC ta dakatar da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, Barrister Hudu Ari daga aiki.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, INEC ta umarci kwamishinan ya fice daga ofishinta har sai abin abin da hali ya yi.

Ta ce daga yanzu sakataren hukumar a jihar Adamawa ne zai karɓi ragamar aiki.

Jami’ar hukumar zaɓen Zainab Aminu Abubakar, ta ce an dakatar da kwamishinan zaɓen ne har sai an kammala bincike, inda daga nan ne INEC za ta bayyana matsayarta kan lamarin.

A ranar Lahadi ne kwamishinan zaɓen Adamawa ya fito ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar tun kafin a kammala tattara sakamako.

Sai dai INEC ta ce matakin da ya ɗauka haramtacce ne, don haka ba za a yi aiki da shi ba.

Manyan Labarai

Shekaru 63 na Nigeria:- Jawabin Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci shugabanni da saura al’umma da suyi koyi da tsaffin shugabannin da suka gabata wajen kawowa ƙasar nan ci gaba da zaman lafiya musamman a irin wannan lokaci.

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yau yayin da yake jawabi kan cikar ƙasar nan shekara 63 da samun kyancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.

 

Gwamna Abba ya kuma ce la’akari da yadda ake tunawa da tsaffin shugabanni wajen ciyar da ƙasar nan gaba ya kamata su shugabannin yanzu suyi koyi da su.

 

 

Ka zalika ya ƙara da cewa ya kamata shugaban ni su tabbata sun yiwa al’umma abin da suke buƙata domin tabbatar adalci.

 

Gwamnatin tace zata ci gaba da gudanar da aikin ta kamar yadda ta tsara domin ciyar da Kano gaba.

Continue Reading

Hangen Dala

Hukuncin Kaduna :- PDP za ta daukaka kara

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ta tabbatar da zaben Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC, inda ta ce za ta garzaya kotun daukaka kara.

Alberah Catoh, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a a Kaduna.

Catoh ya ce, wani nazari da lauyan PDP ya yi ya nuna cewa hukuncin bai cika wasu ka’idoji na tabbatar adalci ba.

Martanin ya zo ne sa’o’i bayan kotun da ke zamanta a Kaduna ta amince da nasarar zaben Sani.

Ya kara da cewa hukuncin bai dace da wasu dokoki da ka’idojin zabe ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda haka jam’iyyar ta umurci lauyoyinta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara da ke Abuja a cikin wa’adin da doka ta kayyade.”

Catoh ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar PDP a fadin jihar da su kwantar da hankalinsu tare da nuna kwarin gwiwarsu kan lamarin.

Continue Reading

Hangen Dala

Abba ya biyawa Daliban Kano kudin makaranta

Published

on

Abba Kabir ya biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero, waɗanda ba su samu damar biya ba, kimanin Naira Miliyan ɗari bakwai.

 

Sakataren hukumar bayar da tallafin ilimi ta jihar Kano, Hon. Kabir Getso Haruna ne, ya bayyana hakan a ranar Talata.

 

Yana mai cewa, “Yanzu haka Gwamnatin Kano, ta biya wa ɗalibai ƴan asalin jihar, dubu bakwai kuɗin makarantar”.

 

Ya kuma ce, “Daga yau Talata, dukkan ɗaliban, su tafi Jami’ar Bayero, tsangayoyin su, domin ƙarasa rijista na shekarar 2023, su ci gaba da karatu”. Inji Hon. Kabir Getso.

Continue Reading

Trending