Connect with us

Manyan Labarai

Kano zata buɗe wasan farko na kakar wasannin NLO ta bana

Published

on

Nationwide League One

Mahukunta shirya gasar ajin ƙwararru mataki na biyu a ƙasa wato ‘Nationwide League One (NLO), sun tabbatar da  jihar Kano a matsayin birnin da za a fara take gasar kakar wasannin ta bana 2023/22.

Babban jami’in yaɗa labaran gasar ta ƙasa Abdulgafar Oladimeji ne ya bayyana haka a Asabar 22 ga Afrilu 2023, a Kano ya yin ganawar sa da manema labarai.

Sabon jami’in yaɗa labaran na NLO, ya ce za a fara gasar a ranar 04 ga watan Mayu a cibiyoyin ƙasar nan da aka ware na shiyya shiyya guda 8, inda jihar Kano take da rukuni biyu da za a fafata a gasar a filayen Sani Abacha dake Kofar Mata sai na Kano dake Sabongari.

” Ina son na tabbatar muku dacewa zaku ga sabuwar gasa da ta banbanta da sauran na baya domin wannan karo tsari take da shi na musamman”

” Bugu da ƙari an shigo da Kamfanoni da zasu dau nauyin gasar da hakan zai taka gagarumar rawa , kana a ɓangare ɗaya gasar zata samu gagarumar yayatawa daga wajen kafafen yaɗa labarai” inji Abdulgafar Oladimeji.

Kungiyar Bournemouth ta sayi dan wasan kasar Ghana Semenyo

Daga cikin wasu daga cibiyoyin da za’a gudanar da gasar sun haɗa da , filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna sai na Zaria , kana na Pantami a jihar Gombe da na Karkanda dake Katsina , haka zalika filin wasa na Giginya dake Sokoto da Kontagora a jihar Niger ciki har da na Lafia a jihar Nassarawa sai na August 04 dake Damaturu a jihar Yobe.

Za’a fara wasan na farko a tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta matasa ta Kano Pillars wato Junior Kano Pillars , da abokiyar karawar ta ta Kwankwasiyya FC, tsohuwar tawagar Samba Kurna.

Manyan Labarai

Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Abba Gida Gida ya fara rusau

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta fara rushe wasu gine gine da aka yi su a wuraren gwamnati Ba bisa ka’ida ba.

A cikin daren Asabar din nan ne tawagar Kwamitin kar ta kwana mai lura da rushe gine gine ta fara da rushe wani sabon rukunin shaguna mai kunshe da sama da shaguna 90 dake jikin filin sukuwa a jihar Kano.

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Ahmad Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewar wannan aiki somin tabi ne domin batun rushe gine ginen da aka yi su akan filayen jama ar Kano lamari ne da babu gudu babu ja da baya kamar yadda gwamna Engr Abba Kabir Yusif ya bayyana a lokacin da yake yakin neman zabe.

Tawagar kwamitin na kar ta kwana zai cigaba da rushe dukkan wasu gine gine da aka yi su ba bisa kaida ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

An bukaci a kama Ganduje

Published

on

Wata kungiya me rajin tabbatar da adalchi Mai suna War against Injustice ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ta kama tare da bincike hadi da gurfanar da tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a gaban kuliya bisa zargin faifen videon Dala da aka zarge shi a shekarar 2018.

Cikin wata takarda da Mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar kwamred Umar Ibrahim Umar tace binciken shine kadai zai Sanya al’ummar Kano su samu nutsuwa wajen cigaba da yakar cin hanci da rashawa.

Kazalika kwafin takardar an Kuma Kara gabatar da shi ga hukumar yakar rashawa da dangogin su ta ICPC domin itama ta taimaka wajen gudanar da wancan bincike.

Continue Reading

Trending