Connect with us

Manyan Labarai

Tallafawa mabuƙata zai rage musu raɗadin rayuwa -Sharif Abdulkareem Almagili

Published

on

Sarkin sharifan jihar Jigawa

Sarkin Sharifan jihar Jigawa Sayyadi Sidi Sharif Muntaƙa, ya shawarci al’umma da su ƙara haɗa kai domin tabbatuwar zaman lafiya a kasar nan.

Sarkin Sharifan ya bayyana hakan ne a yayin taron haɗin kan mutane tare da lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, wanda ƙungiyar haɗin kan Sharifai ta Mu’assatul Muhammad Bin Abdulkareem Almagili Altilmizani Aljazairi ta gudanar cikin unguwar Sharifai Zauren Tudu a ranar Asabar.

Sayyadi Sidi Sharif Muntaƙa ya kuma ƙara da cewa, bai kamata sharifai da sauran al’umma su rinƙa bari ana rarraba kan su ba, domin kuwa hakan kan kawo koma baya a tsakanin al’umma, inda ya ce haɗin kan Sharifai da sauran al’umma shine babban burinsu a rayuwa.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar ta Mu’assasa, kuma Galadiman Sharifan ƙasar nan Sharif Abdulkarim Sharif Ali Salihu Almagili, ya ce lalubo hanyoyin haɗin kan Sharifan ƙasar nan da sauran al’ummar musulmi, da tallafawa marayu da mabuƙata ne ya sanya suka suka ƙirƙiri ƙungiyar.

“Mawadata ku ƙara ƙaimi wajen tallafawa marasa shi domin rage musu wani raɗadin rayuwa da yake damunsu na yau da kullum, “in ji Sharif Abdulkarim”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar taron ya samu halartar Sharifai da dama da sauran al’umma, wanda a yayin taron ƙungiyar ta ƙaddamar da Fom ɗin zama ɗan ƙungiyar.

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisa ta amince da dokar gwajin cutar Ƙanjamau da ta Sikila kafin aure a Kano

Published

on

Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Har ila yau, dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Continue Reading

Trending