Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta sake Bude asibitin Hasiya Bayero

Published

on

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sake buɗe Asibitin yara na Hasiya Bayero.

Da yake jawabi yayin buɗe Asibitin, Gwamna Abba Kabir ya zargi gwamnatin baya da sayar da Asibitin, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin wahala.

A cewar sa, hakan ta sanya ya ci alwashin idan ya zama gwamnan Kano sai ya ƙwato wa al’umma kayan su.

“Duk da irin roƙon da al’umma su ka riƙa yi, amma gwamnatin da ta gaba ta sayar da wannan asibiti, Wanda dalilin hakan al’umma suka rika shan wahala, su ka riƙa zuwa neman Asibitocin yara masu tsada kuma ba lallai suna da ingancin wannan ba.”

“Da mu ka ga haka, sai mu ka ci alwashin kwatowa al’umma asibitin su, yau ga shi mun cika alƙawari, muna cikin farin ciki da alfahari da wannan gagarumin aikin,” in ji gwamna Abba.

Ya ce Asibitin yana ɗauke da gadaje 86, kuma an saka masa kayayyakin aiki na zamani da za a rika kula da lafiya cikin inganci da sauƙi.

Ya kuma ja kunnen jami’an lafiya na Asibitin da su kula da gudanar da ayyukan su, inda ya gargaɗe su a kan yin fashi da makara, inda ya ce “gwamnati ba za ta lamunci sakaci da aiki ba.”

A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin da ya yi na sake buɗe Asibitin.

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Manyan Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi! Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakin sa da ƴan majalisar jihar na watanni 6.

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, da mataimakiyar sa Mrs. Ngozi Odu, har na tsawon watanni 6.

Shugaba Tinubu ya bayyana daukar matakin ne a cikin wani taƙaitaccen jawabin sa da ya gabatar a cikin daren Talatar nan, ya ce ya yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen sanya wannan doka wacce ta kwace mulkin jihar daga hannun gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakin sa har sai lamura sun dawo dai-dai a jihar.

Kazalika, shugaba Tinubu ya kuma bayyana dakatar da dukkanin ƴan majalisar dokokin jihar suma na tsawon watanni shidan, tare da sanya dokar ta ɓaci a jihar.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rikicin siyasar da ya daɗe da kunno kai a tsakanin gwamna Fubara da ministan birnin tarayya Abuja Nyesome Wike, al’amarin da ya janyo takun saƙa tsakanin sa da ƴan majalisar dokokin jihar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Isra’ila ta kashe sama da mutane 200 bayan karya yarjejeniyar tsagaita Wuta a Gaza

Published

on

Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, tare da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasdinawa.

Jaridar TRT Hausa ta ruwaito cewa, aƙalla Isra’ila ta kashe fiye da mutum 200 tare da jikkata ɗaruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti, kamar yadda majiyoyin wani asibiti a yankin Gaza suka bayyana.

Continue Reading

Trending