Connect with us

Manyan Labarai

Jerin ma’aikatun Ministocin Tinubu

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya baiwa Mutum 45 cikin 47 da majalisar dattawa ta tantance kuma ta tabbatar a matsayin ministoci maaikatun su.

 

Ga jerin sunayen ministcoin da ma’aikatunsu:

 

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin na Dijita – Bosun Tijani

Ƙaramin Ministan Muhalli – Ishak Salaco

Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki – Wale Edun

Ministar Harkokin Teku da Tattalin Arziki – Bunmi Tunji

Ministan Lantarki – Adedayo Adelabu

Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma – Tunji Alausa

Ministan Ma’adanai – Dele Alake

Ministan Yawon Buɗe-Ido – Lola Ade-John

Ministan Sufuri – Adegboyega Oyetola

Ministan Kasuwanci da Zuba Jari – Doris Anite

Ministan Wasanni – John Enoh

Ministan Abuja – Nyesom Wike

Ministar Al’adu – Hannatu Musawa

Ministan Tsaro – Muhammad Badaru

Ƙaramin Ministan Tsaro – Bello Matawalle

Ƙaramin Ministan Ilimi – Yusuf T. Sununu

Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane – Ahmed M. Dangiwa

Ƙaramin Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane – Abdullah T. Gwarzo

Ministan Kasafi da Tsare-Tsare – Atiku Bagudu

Ministan Muhalli (Kaduna)

Ƙaramar Ministar Abuja – Mairiga Mahmud

Ministan Albarkatun Ruwa – Bello M. Goronyo

Ministan Noma da Samar da Abinci – Abubakar Kyari

Ministan Ilimi – Tahir Maman

Ministan Harkokin Cikin Gida – Sa’Idu A. Alkali

Ministan Harkokin Waje – Yusuf M. Tuggar

Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a – Ali Pate

Ministan Harkokin ‘Yan Sanda – Ibrahim Geidam

Ƙaramin Ministan Ƙarafa – U. Maigari Ahmadu

Ministan Ƙarafa – Shuaibu A. Audu

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai – Muhammed Idris

Ministan shari’a – Lateef Fagbemi

Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyuka – Simon B. Lalong

Ƙaramar Ministar Harkokin Cikin Gida – Imaan Sulaiman-Ibrahim

Ministan Ayyuka na Musamman – Zephaniah Jisalo

Ministan Albarkatun Ruwa – Joseph Utsev

Ƙaramin Ministan Noma da Samar da Abinci – Aliyu Sabi Abdullahi

Ministan Kimiyya da Fasaha – Uche Nnaji

Ƙaramar Ministar Ƙwadago da Samar da Ayyuka – Nkiruka Onyejeocha

Ministar Harkokin Mata – Uju Kennedy

Ministan Ayyuka – David Umahi

Ministan Sufurin Jiragen Sama – Festus Keyamo

Ministan Matasa – Abubakar Momoh

Ministar Agajin Gaggawa da Rage Talauci – Betta Edu

Ƙaramin Ministan Albarkatun Iskar Gas -Ekperikpe Ekpo

Ƙaramin Ministan Man Fetur – Heineken Lokpobiri.

Za dai a rantsar dasu ne a ranar 21 ga watan Agustan da muke ciki a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Manyan Labarai

Uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a Kano sun rasu

Published

on

Rahotanni da dumi-ɗumin sa na bayyana cewar yanzu haka uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a unguwar Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano sun rasu.

Wani mazaunin garin ya shaidawa Dala FM Kano, da tsakar ranar Larabar nan cewar, daga cikin mutane ukun da suka rasu har da limamin da ya jagorancin sallar asubar wannan rana, wanda a lokacin ne matashin ya cinna musu wutar lamarin da jikin su mutanen sama da 20 ya sassaɓule.

Idan dai ba’a manta ba matashin ya cinnawa mutanen wuta ne bayan da ya watsa Fetur cikin masallacin yayin da suke tsaka da sallar Asubah, ta wannan rana, wanda tuni jami’an tsaron ƴan sanda suka cika hannun su da shi.

Matashin dai ya ce ya cinnawa mutanen wutar ne biyo bayan wata magana da suke faɗa masa wanda ransa baya daɗi, ina ya sayo Fetur a cikin wani Galan lamarin da yaje ya kunna musu wutar, duk da shima hannayen sa biyu sun ƙone.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun kama matashin da ya kunnawa mutane sama da 20 Wuta a cikin wani masallaci – Ƴan Sandan Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi da ake zargi da cinnawa wasu mutane Wuta, a lokacin da suke tsaka da Sallar Asubar yau Laraba, a cikin wani Masallaci a garin Larabawar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM Kano, a yau Laraba, ya ce bayan samun rahoton faruwar al’amarin ne Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya tura tawagar jami’an su inda suka kai ɗaukin gaggawa.

Matashin da ake zargin mai suna Shari’u Abubakar ɗan shekaru shekaru 38, ya ce shine ya siyo Fetur ya kunna wutar inda ya wurgata a cikin masallacin, lamarin da ya sa mutane da dama suka ƙone a sassan jikin su.

“Aƙalla mutane 24 ne suka ƙone bayan da matashin ya kunna musu wutar a cikin masallacin, wanda tuni jami’an mu suka kai su asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, inda suke ci gaba da samun kulawar likitoci, “in ji SP Kiyawa”.

Koyawa, ya kuma ce daga binciken farko da suka fara matashin ya tabbatar da cewa shine ya sayo Mai a gidan Mai a cikin wata roba, yazo ya kunna wutar, biyo bayan wani rikicin gado da a tsakanin sa da wasu daga cikin mutanen yankin su, inda shima hannayen sa biyu suka ƙone.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sama da mutane 20 ne suka ƙone a sassan jikin su bayan da ake zargin wani abu ya fashe a cikin wani masallaci da ke Kano

Published

on

Rahotanni na nuni da cewa an yi zargin fashewar wani abu da asubahin wannan rana ta Laraba, a garin larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar kano, wanda kuma ya jikkata sama da mutane 20, sakamakon ƙonuwa a sassan jikinsu.

Yanzyu haka dai da yawa daga cikinsu sun fara karɓar agajin
gaggwa a babban asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, da ke Kano, kamar yadda wani ganau ya shaidawa
gidan rediyon Dala FM, lokacin da ya ziyarci asibitin a safiyar wannan
rana.

Sai dai wani da ya tsallake rijiya da baya mai suna Yusuf Abdullahi, ya ce yana cikin masallacin lokacin da lamarin ya faru suna tsaka da Sallah Asuba aka kunna wutar daga waje inda aka cillota cikin masallacin, saɓanin abin fashewar da wasu suke faɗa.

Ya kuma ce, “Allah ne kawai ya bani ikon fita Amma mutane da yawa ciki har da yan uwana guda biyu lamarin ya rutsa da su, kuma wutar ta yi musu illa babba saboda ko kasan mutum wallahi idan ka gan shi wallahi ba za ka iya gane shi ba”. Inji Yusuf Abdullahi”.

Wakilin Dala FM, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki, ya tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar tarho, sai dai ya ce yanzu haka
yana kan aikin tattara bayanai akan al’amarin, wanda rundunar
za ta fitar nan gaba kaɗan.

Continue Reading

Trending