Connect with us

Manyan Labarai

Ƙungiyar Ja’en Facebook Connect ta raba katin magani kyauta cikin Asibitoci a Kano

Published

on

Shugaban riƙo na ƙungiyar masu amfani da shafukan sada zumunta wato Ja’en Facebook Connect Auwal Abdullahi mai Walda, ya ce matsawar gwamnati ta samar da hanyoyin dogaro da kai ga matasa, babu makawa matasan zasu gujewa faɗawa mawuyacin hali.

Auwal Mai Walda Ja’en ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakilinmu na ƴan Zazu, lokacin da yake ƙarin bayani kan tallafin katin magunguna da ƙungiyar su ta bayar a ƙananan Asibitocin garin, domin sauƙaƙawa marasa lafiya.

Ya kuma ce bai kamata matasa su rinƙa wasa da lokacinsu ba, domin kuwa sune ƙashin bayan al’umma.

Ya kara da cewa matsin rayuwar da ake ciki a halin yanzu ya sanya suka zamar da katin magungunan guda 1200, domin ragewa al’umma musamman marasa lafiya wani raɗaɗin rayuwa dake damunsu.

Manyan Labarai

Matsalar Tsaro: Ƴan Daba sun sake kashe mutane biyu a Ɗorayi – Ɗan Fodiyo

Published

on

Wasu matasa da suka addabi unguwar Ɗorayi da faɗan Daba, da sace-sacen kayayyakin jama’a, sun sake lashe aƙalla Mutane biyu bayan da suka hau su da sara da makamai.

Shugaban babban kwamitin Tsaro na unguwar Ɗorayi a jihar Kano Dakta Abdullahi Idris Ɗan Fodiyo, ne ya bayyanawa tashar Dala FM Kano, a ranar Asabar, ya ce, kashe mutane biyun ya biyo bayan yadda wasu tarin matasa suka shiga yankin a daren Alhamis da kuma Juma’ar da suka gabata, riƙe da makamai inda suka rinƙa yin abinda bai kamata ba.

“Lokacin da matasan suka shigo yankin namu riƙe da muggan makamai sun shiga shagon wani mai canji Waya inda suka kwashe Wayoyi guda 115 na mutane da suka kai masa Caji suka gudu dasu kuma har yanzu basu dawo dasu ba, “in ji Ɗan-Fodiyo”.

Malamin ya kuma ce matuƙar ana so a kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar unguwar ta Ɗorayi, sai kowa ya bada gudunmawar sa, suma masu shaguna a yankin sai sun rinƙa ajiye makaman da za su rinƙa kare kan su daga matasan da suke addabar su.

Ɗan Fodiyo, ya ƙara da cewa akwai buƙatar a ƙara yawan jami’an tsaro a yankin na Ɗorayi, domin ganin an magance matsalar tsaron da taƙi ci taƙi cinyewa a unguwar.

Majiyar Dala FM Kano, ta rawaito cewa wannan na zuwa ne bayan da wasu tarin matasa suka addabi al’ummar unguwar Ɗorayi da kewaye da faɗa Daba, gami da sace-sacen kayayyaki, al’amarin da ke sanya furgici a zukatan jama’ar yankin.

Continue Reading

Manyan Labarai

Yadda mazauna Gayawa a Kano suka gudanar da gangami akan rashin kyan hanyoyi

Published

on

Al’ummar unguwar Gayawa da kewaye da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano, sun gudanar da wani gangami domin nuna damuwar su kan matsalar rashin kyan hanyoyi da suke fama dasu a yankunan su.

Ɗaruruwan mazauna unguwar ta Gayawa da kewaye ne dai suka fito a ranar Asabar, tare da neman ɗaukin mahukunta, kan su gyara musu titunan yankunan su da suka haɗar da na Gayawa, da titin Badaru, da na gadar Getsi, da titin na Tsahare, da kuma Jaba, da na Rimin Keɓe.

Da yake zantawa da Dala FM Kano, jagoran mutanen da suka fito gangamin mai suna Haruna Musa Isma’il, ya ce sun fito ne domin sanar da gwamnatin jihar Kano, da dukkanin shugabanninn yankunan su matsalar rashin hanyoyin da ta daɗe tana damun su shekara da shekaru.

A cewar sa, “Mun daɗe muna bibiyar mahukunta halin da muke ciki amma kawo yanzu ba’a share mana hawayen mu ba a don haka ne ma muka fito domin mu nusartar da gwamnatin halin da muke ciki don a kawo mana ɗauki, “in ji Haruna Musa”.

Anasa ɓangaren wani matuƙin baburin Adai-dai Sahu a yankin, ya shaidawa Dala FM Kano, cewa har mata biyu ne suka taɓa Haihuwa a cikin baburi ɗin sa, lokacin da zai kai su Asibiti, bisa rashin kyan hanya.

“Baya ga batun rashin kyan hanyoyi da muke fama dasu akwai kuma rashin Kwalabati da yake damun mu, wanda ida akayi ruwan sama yake shiga cikin gidajen jama’a, “in ji shi”.

Al’ummar unguwar ta Gayawa da kewaye da ke ƙaramar hukumar Ungog a jihar Kano, sun kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da shugabannin su na ƙaramar hukumar tasu, da su kawo musu ɗauki wajen gyara musu hanyoyin su da suka lalace, bisa yadda suke matuƙar shan wahala.

Continue Reading

Manyan Labarai

An kama mutumin da ake zargi da damfarar wasu mata wajen karɓar musu kuɗaɗe da zummar zai samar musu aiki a Kano

Published

on

Rundunar tsaro ta Civil Defense a nan Kano ta kama wani mutum da zargin laifin damfarar wasu mata wajen karɓar kudadensu da sunan zai samar musu aiki a wasu hukumomin gwamnati da na tsaro.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SC Ibrahim Idris Abdullahi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Dala FM a ranar Laraba.

Ya ce mutumin mai suna Mu’azu Muhammad Ibrahim, da ke unguwar Sagagi sun kamashi ne sakamakon korafe – korafen da suka samu daga wasu mata da suka bayyana musu cewa, ya karbi kudinsu sama da Naira miliyan ɗaya da dubu dari ɗaya da sunan zai nemar musu aiki, duk da bashi da damar hakan.

“A lokacin da jami’an mu suka binciki mutumin ya shaida musu cewa tabbas ya karɓi wadannan kuɗaɗen a wajen matan da summar zai samar musu aikin amma kuma al’amarin ƙarya ne bashi da takardun samar da aiki ko hanyar su, “in ji SC Ibrahim”.

SC Ibrahim ya kuma ƙara da cewa da zarar rundunar ta kammala binciken ta akan wanda ake zargi zata gurfanar dashi a gaban Kotu.

Da yake nasa jawabin mutumin da ake zargin mai suna Mu’az Muhammad Ibrahim, ya tabbatar da karɓar kuɗaɗen sai dai ya ce wasu kuɗaɗen suna hannun wata mata, amma dai ya yi nadama ba zai ƙara ba.

“Aƙalla watanni shida ke nan da fara bayar da kuɗaɗen nasu, abinda muka yi ba dai-dai ba ne kuma muna neman afuwa akai ba zamu sake ba, “in ji mutumin”.

Rundunar Civil Defense ɗin a jihar Kano, ta kuma ja hankalin al’umma da su rinƙa yin taka-tsantan tare da lura da irin mutanen da suka ce za su samar musu aiki, domin gujewa faɗawa komar ɓata gari.

Continue Reading

Trending