Connect with us

Siyasa

Ina da yakinin nasara a Kotun Ƙoli – Gwamnan Kano

Published

on

Yayin da yake jawabi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan yadda alkalan kotun koli za su iya tabbatar da adalci kan karar zaben gwamnan jihar da ke gaban kotun kolin.

Bayanin hakan na cikin wani rahoton kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN, wanda yayi nuni da cewa, Yusuf ya bayyana hakan ne a filin wasa na Sani Abacha a jiya Lahadi, yayin bikin kaddamar da rundunar jami’an tsaro 2,500 da makarantar horas da jami’an tsaro za ta horas da su a Kano, domin bada tsaro.

A cewarsa, “Muna da yakinin cewar alkalan kotun koli za su yi mana adalci ga daukaka karar da ke gabansu, don haka mutanen Kano su kwantar da hankalinsu,” in ji Abba Kabir”.

Gwamnan Kano ya kuma bayyana cewa an kafa makarantar horar da jami’an tsaron ne a zamanin gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso, da nufin horas da matasa kan harkokin tsaro a Kasa.

Yusif ya kuma kara da cewa an zabo wadanda aka horas da su ne daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano, kuma za’a dauke su aiki tare da tura su ga ma’aikatun gwamnati daban-daban da zarar sun kammala daukar horo a makarantar.

A cewar sa, wadanda suka ci gajiyar shirin za’a samar musu da ayyukan yi a ma’aikatu na jiha da kuma kananan hukumomi 44.

Jaridar Daliy Nigerian Hausa ta rawaito gwamna Yusuf ya yaba da goyon bayan da mazauna Kano suke ba su, inda ya kuma bukace su da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda da son zaman lafiya a Kasa.

Hangen Dala

Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.

Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.

Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.

Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.

Continue Reading

Labarai

Da Dumi Dumi:- EL Rufai ya kai karar majalisar dokoki

Published

on

Tsohon Gwamna jahar Kaduna Mal. Nasir elrufai ya Maka majalisar Dokokin jahar Kaduna a gaban Kotu a bisa bata Masa Suna da majalisar tayi na cewa Gwamnatin sa ta sace kudaden jahar da Suka naura naira miliyan dubu Dari Hudu.

Tsohon Gwamna ya shigar da karar ce, a Gaban babbar kotun taraiyya dake NDA Kaduna a safiyar Laraban nan 26 ga watan Yuni 2024.

Inda ya bukaci Kotun data tursasa majalisar ta bashi hakuri a bainar jama’a, sakamakon Kazafin da Yan majalisan Suka yi masa da mukarraban Gwamnatinsa data gabata.

 

Karin bayani na nan tafe….

Continue Reading

Siyasa

Zauren jam’iyyun haɗin kan kasa IPAC sun cire shugaban jam’iyyar LP na Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su 

Published

on

Sakataren zauren jam’iyyun haɗin kan kasar nan, IPAC na ƙasa reshen jihar Kano, kuma shugaban jam’iyyar APM na Kano Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire shugaban jam’iyyar LP na jihar Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su ta IPAC, baki ɗaya.

Sakataren na IPAC, Nuhu Idris ya ce sun dauki wannan mataki ne bisa yadda Rajin ke amfani da kungiyar CUPP, da rusassun jam’iyyun kasar nan suka samar a baya, a dan haka, duk wata jam’iyyar dake da rijista a yanzu na ƙarƙashin IPAC.

Ya kuma ce dokar da ta kafa IPAC, ba ta bai wa ɗan kowacce jam’iyya damar shiga hurumin wata jam’iyyar ba kamar yadda Rajin ke ƙoƙarin yi a rikicin dake faruwa a jam’iyyar APC a nan jihar Kano.

Shugaban jam’iyyar APM, ɗin Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire Rajin daga tafiyar ta IPAC ne, sakamakon wata sanarwa da ya fitar, ya ce, ka da hukumar zaɓe INEC, ta yi watsi da shugaban mazaɓar Ganduje, wanda hakan ba dai-dai ba ne a dokance, dan haka, suka fitar da shi daga cikin tafiyar tare da sanar da shugabancin jam’iyyar sa na kasa.

Continue Reading

Trending