Connect with us

Manyan Labarai

Likin kudi a wajen Biki ya janyowa ƴar Film dauri a gidan yari.

Published

on

Wata kotu ta yanke wa wata ƴar Film ɗin Najeriya, hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari, bayan da aka ɗauki hotonta tana liƙa sabbin takardun kuɗin Naira da aka fitar a bara, tare kuma da taka su a cikin mutane.

‘Yar Film din dai mai suna Oluwadarasimi Omoseyin, an kamata ne a watan Fabrairun da ya gabata a Legas, bayan fitar fai-fan bidiyon ta a wurin wani biki da ya bayyana a intanet tana likin kudin.

Majiyar BBC ta rawaito cewa an kuma nuna ƴar fim din tana albazaranci da sabbi kuɗaɗen tana likawa a wajen bikin.

Yayin da aka gurfanar da ita a gaban kotun, da farko, ta ƙi amsa laifin da ake tuhumar ta da shi, amma daga bisani ta amsa laifin da aka tuhume ta da shi.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, ta ce an ɗauki bidiyon tauraruwar ne da kuɗi kimanin Naira 100,000 a lokacin da take liƙawa wajen daurin auren abokiyarta, a unguwar Lekki da ke birnin Legas, shekara daya da ta gabata.

A jawabinta ga hukumar, Omoseyin ta ce ta karbi sabbin takardun Naira ɗin ne daga wajen masoyanta a wurin bikin kuma ba ta san wadanda suka ba ta kudin ba ma.

Sai dai kuma a lokacin da ta bayyana a gaban kotu a ranar Alhamis, Omoseyin ta amsa laifinta bayan wasu “shaidu masu ƙarfi” da ake tuhumar ta da su, kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin X.

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle ofishin kamfanin jiragen sama na Max Air da na Ɗantata and Sawoe a jihar

Published

on

Gamnatin jihar Kano ta rufe ofishin kamfanin sufurin jiragen sama na Max air da na Dantata and Sawoe a nan Kano, sakamakon harajin da take bin kamfanonin.

Shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Kano Dakta Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan kulle kamfanonin biyu a ranar Litinin.

Zaid, wanda Daraktan Bibiyar bashi da tursasawa wajen karɓo bashin harajin da Gwamnatin Kano ke bi, Ibrahim Abdullahi ya wakilta, ya ƙara da cewar hukumar ta tattara haraji ta jihar Kano tabi duk matakan da ya kamata kafin daukar wannan matakin.

“Dole ce ta sa hukumar ɗaukar wannan mataki na rufe kamfanonin da wuraren da ke gujewa biyan haraji a jihar Kano, “in ji Ibrahim Abdullahi”.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar hukumar ta ce za ta ci gaba da bun duk matakan doka akan masu ƙin biyan harajin a fadin jihar Kano.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta hana duk wata kafar yada labarai yin labarin da ya shafi Auwalu Danladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 4 karkashin jagorancin mai Shari’a Usman Na Abba ta yi hani ga duk wasu Jami’an Ƴan sanda ko na duk wata hukuma ta daban daga gayyata ko tsangwama, ko kuma bincike ko kamawa, ta kowace siga ga kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa Auwalu Ɗanladi Sankara.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kotu ta wanke Auwalu Sankara daga zargin mu’amala ko alaƙa da juna tsakanin mai ƙara da Taslim Baba Nabegu har zuwa lokacin sauraran ƙarar.

Kotun ta kuma amince da rokon da wani lauya mai suna Barrister I.C Ekpinovi ya yi amadadin mai kara Auwalu Danladi Sankara wanda ya yi karar Nasiru Buba.

Mai karar ta bakin lauyansa ya bayyana wa kotun rokonsa inda ya roki kotun da ta dakatar da wanda ake kara ko dai shi da kansa ko kuma ƴan korensa daga ci gaba da yaɗa wata magana wadda wata babbar kotun Shari’ar Muslunci da ke Kano ta rufe.

Mai Shari’a Usman Na Abba ya ayyana cewar ko dai wanda aka yi kara ko yan korensa ko kuma wasu wakilansa, da a dai na yaɗa waccan magana har zuwa lokacin da kotun za ta saurari kowanne ɓangare.

Kotun ta ayyana cewar ta yi hani ga duk wata kafa ta yada labarai ko dai Rediyo ko Talabijin, ko shafukan sada zumunta da kafar Intanet da duk wata kafa wadda take iya sadar da labarai, daga yaɗa labaran da suka shafi Auwalu Ɗanladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

A ranar Talata ne dai gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya bayyana mayar da Auwalu Ɗanladi Sankara muƙamin sa na Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar, bayan da kotu ta wanke shi daga zargin da hukumar Hisbah ta Kano, ta yi masa kan zargin baɗala da wata matar aure.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa kotun ta kuma sanya ranar 28 ga wannan watan na Nuwamba dan sauraron kowane ɓangare akan shari’ar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Zargin Baɗala: Kotu ta wanke Auwalu Sankara da Taslim Baba Nabegu a Kano.

Published

on

Babbar kotun Shari’ar Muslunci mai zaman ta a kofar kudu ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ta sallami dakataccen kwamishina a jihar Jigawa, Auwalu Ɗanladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

Tun da farko kotun ce ta tura ofishin ƴan Sanda Shiyya ta ɗaya da ke jihar Kano, wato Zone 1, domin mukaddashin babban sifetan yansanda ya binciki zargin da ake wa Auwalu Danladi da Taslim Baba Nabegu, sakamakon korafin da wani mutum Mai suna Nasiru Buba ya yi, wanda ya zargi Auwalun da cewar suna yin mu’amalar da bata dace ba.

Cikin ƙunshin takaddar da muƙaddashin babban sifetan ƴansanda ya tura wa kotun ya bayyana cewar, hukumar Hisbah ta yi azarɓaɓi akan batun, kuma ya umarce su da su rinƙa yin aiki a bisa tsarin doka.

A zaman kotun na yau mai Shari’a Sarki Yola ya ayyana cewar babu tuhuma akan waɗanda ake zargin sakamakon yadda ƴan sanda suka gudanar da bincike, inda suka ce sun samu cewar maganar Jita-jita ce kuma Shari’a bata karɓar jita-jita.

Har ila yau, ma’aikatar Shari’a ta jahar Kano ta bayyana cewar babu tuhuma akan waɗanda ake zargin sakamakon rashin gamsassun hujjoji.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ayyana cewar ya sallami Auwalu Danladi Sankara da Taslim Baba Nabegu nan take, kuma kotun ta umarci kowa ya zauna lafiya.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, da yake jawabi lauyan wanda ake ƙara Barrister Saddam Sulaiman, ya ce dama maganar siyasa ce ta shigo cikin al’amarin.

Continue Reading

Trending