Connect with us

Manyan Labarai

Mun sanya tukuicin miliyan 50 ga duk wanda ya bamu bayanan sirrin kama wasu ƙasurguman ƴan ta’adda biyu – Ƴan Sandan Katsina

Published

on

Rundunar ƴan Sandan jihar Katsina ta sanya kyautar kuɗi har Naira miliyan hamsin ga duk wanda ya bata bayanan sirrin kama wasu riƙaƙƙun ƴan ta’adda biyu da suka yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Katsina ASP Abubakar Sadik Aliyu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce mutane biyun da ake nema ruwa a jallo sun yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane a yankin ƙaramar hukumar Ƙanƙara da Safana a jihar ta Katsina.

Sanarwar rundunar ƴan sandan ta ce masu garkuwa da mutanen da ta ke nema ɗin ruwa a jallo, sun yi ƙaurin suna da Modi-Modi, da kuma Jan Kare, dukkanin su Maza.

Rundunar ƴan sandan jihar Katsinan ta buƙaci duk wanda ya samu bayanan sirrin masu garkuwa da mutanen ya kai rahoton sirrin ofishin rundunar mafi kusa, ko kuma ya kira lambar kar ta kwana ta helkwatarta dake jihar akan 07015142112, ko kuma 08023871144.

Hakazalika rundunar ta buƙaci al’ummar jihar da su baiwa jami’an su haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da samar da tsaro.

Manyan Labarai

Zamu ƙone duk kayayyaki marasa inganci da muka kama da zarar an gama shari’u – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta ƙone dukkanin kayayyaki marasa inganci da ta kama, da zarar an kammala dukkanin shari’un da suke a gaban Kotu.

Kwamishinan ma’aikatar ciniki da masana’antu, Adamu Aliyu Kibiya, ne ya tabbatar da hakan, a yayin wata ziyara ta musamman da ya kai hukumar kula da ingancin kayayyaki ta jihar Kano, a yammacin yau Alhamis.

Amadadin Kwamishinan babban sakataren ma’aikatar, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, da zarar an kammala Shari’un da masu kayan za’a ƙone su baki ɗaya.

“A bisa al’adar ma’aikatar ciniki da masana’antu, dama duk sabon Kwamishina idan ya zo yana ziyarartar hukumomin da suke da jiɓi da ma’aikatar domin duba irin aikace-aikacen su da sauran abinda ba’a rasa ba, hakan ya sa ma Kwamishinan ya ziyarci hukumar a yau, “in ji Ɗan-duwa”.

 

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, babban sakataren ya ƙara da cewa, ziyarar da Kwamishinan ciniki da masana’antun Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kai hukumar kula da ingancin kayayyakin, itace ta farko.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Trending