Manyan Labarai
Matsin Rayuwa: Mutane sun fasa rumbun ajiyar abinci tare da yin awon gaba da su a Abuja
Yayin da al’umma ke cikin matsin rayuwa yanzu haka jama’ar gari sun fasa wani rumbun ajiyar hatsin gwamnati da ke Abuja, inda suka wawushe kayan abincin da ke cikin sa.
Rahotanni sun bayyana cewa tun da sanyin safiyar Lahadin nan ne bata-garin suka yi dirar mikiya inda suka fasa rumbun ajiyar abincin da ke garin Gwagwa, suka rinƙa yin awon gaba da hatsin ciki domin rage wani raɗaɗi.
A zantawar manema labarai da wasu mazauna yankin sun ce, masu jidar kayan abincin sun isa rumbun ajiyar abincin da ke yankin Tasha ne da misalin karfe 7 na safe, suna kinkimo buhunan abincin da ke dauke da tambarin Gwamnatin Tarayya.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa wani mazaunin unguwar Karmo da ke kusa da wurin mai suna Ja’afar Aminu, ya ce an shafe sama da awa biyu ana kwasar kayan abinci daga dakin ajiyar, inda suke yin gaba da shi.
“Mazauna Karmo da makwabtansu daga yankin Jiwa suna tururuwar zuwa kwasar abincin, lamarin da ya haifar da cinkoson ababen hawa a kan hanyar Gwagwa zuwa Karmo zuwa Jabi da Dei-Dei, “in ji mazaunin yankin”.
Hakazalika, Ja’afar ya ce shi kansa yi ƙoƙarin zuwa wurin amma ya hakura, saboda raunukan da ya samu a yamutsin ɗibar kayan abincin a Abuja.
Shima da yake ƙarin bayani kan al’amarin, wani mazaunin Karmo, Christopher Agbo, ya ce wasu daga cikin dandazon mutanen da suka yi wa wurin dirar mikiya sun rinƙa yin awon gaba da ƙarafunan da ke wurin da sauran kayan gwangwan suna tafiya da su.
Idan dai ba’a manta ba irin haka ta faru da kayan tallafin a lokacin annobar COVID-19 a Abuja, inda bata-gari suka far wa rumbuna ajiyar suka yi gaba da su.
Tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa ko a bayan nan ma an gano yadda wasu mutane suka rinƙa jidar kayan abinci a manyan motocin Tirela jahohi daban-daban na ƙasar nan, suna yin awon gaba da su, a wani ɓangare na rage halin matsin rayuwar da suka samu kasu a ciki a ƙasar nan.
Manyan Labarai
Zamu ƙone duk kayayyaki marasa inganci da muka kama da zarar an gama shari’u – Gwamnatin Kano
Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta ƙone dukkanin kayayyaki marasa inganci da ta kama, da zarar an kammala dukkanin shari’un da suke a gaban Kotu.
Kwamishinan ma’aikatar ciniki da masana’antu, Adamu Aliyu Kibiya, ne ya tabbatar da hakan, a yayin wata ziyara ta musamman da ya kai hukumar kula da ingancin kayayyaki ta jihar Kano, a yammacin yau Alhamis.
Amadadin Kwamishinan babban sakataren ma’aikatar, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, da zarar an kammala Shari’un da masu kayan za’a ƙone su baki ɗaya.
“A bisa al’adar ma’aikatar ciniki da masana’antu, dama duk sabon Kwamishina idan ya zo yana ziyarartar hukumomin da suke da jiɓi da ma’aikatar domin duba irin aikace-aikacen su da sauran abinda ba’a rasa ba, hakan ya sa ma Kwamishinan ya ziyarci hukumar a yau, “in ji Ɗan-duwa”.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, babban sakataren ya ƙara da cewa, ziyarar da Kwamishinan ciniki da masana’antun Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kai hukumar kula da ingancin kayayyakin, itace ta farko.
Manyan Labarai
Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.
Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.
Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.
“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.
Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.
Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.
Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.
Manyan Labarai
Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli
Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.
Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.
Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.
A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su