Connect with us

Manyan Labarai

Ɓarawo ya faɗo mana gida kwatsam da mugun makami, Mun yi kururuwa amma shiru – Mazauna Ja’en.

Published

on

Al’ummar unguwar Ja’en layin Shago tara Maƙabarta dake ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, sun shiga tashin hankali da firgici bayan da wasu matasa riƙe da muggan makami suka biyo wani matashi, dake riƙe da Adda a hannunsa, inda ya shiga cikin wani gida ya kulle shi da mazauna gidan, wanda ya shafe kusan awanni uku a cikin ɗakin gidan.

Wata matashiya mazauniyar gidan da lamarin ya faru ta shaidawa wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u cewar, suna zaune suka ga shigowar matashin riƙe da Adda a hannunsa bayan da ya kulle ƙofar gidan, inda su kuma matasan da suka biyo shi suka rinƙa dukan ƙofar da makamai har suka ɓalla ƙofar da summar za su kashe shi, kasancewar ya kulle ƙofar ɗakin da ya shiga hakan ya sa suka yi gaba

Ta ci gaba da cewa, “Mun shafe aƙalla awanni uku muna cikin gidan kuma mun sanar da ƴan sandan Sharaɗa, da na Anty Daba ta wayar tarho, amma ba su zo ba duk da tsawon awannin da muka shafe a daren Lahadi, “in ji matashiyar”.

Ahmad Isma’ila Muhammad, shine kwamandan ƙungiyar Bijilante na unguwar Ja’en layin Shago tara One I, dake ƙaramar hukumar Gwale a Kano, ya ce a lokacin da matashin yake neman gurin tsira sai da ya sari mutane uku a kan hanya, inda ya ce za su ci gaba da bada gudunmawa domin kawar da matsalar tsaro a yankin.

Wakilin namu ya tunubi kakakin rundinar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta wayar tarho, a daren Lahadin ya ce zai bincika, ya kuma ƙara kiransa yau Litinin tare da aike masa saƙon karta kwana amma zuwa yanzu ba muji daga gareshi ba.

Manyan Labarai

Zamu ƙone duk kayayyaki marasa inganci da muka kama da zarar an gama shari’u – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta ƙone dukkanin kayayyaki marasa inganci da ta kama, da zarar an kammala dukkanin shari’un da suke a gaban Kotu.

Kwamishinan ma’aikatar ciniki da masana’antu, Adamu Aliyu Kibiya, ne ya tabbatar da hakan, a yayin wata ziyara ta musamman da ya kai hukumar kula da ingancin kayayyaki ta jihar Kano, a yammacin yau Alhamis.

Amadadin Kwamishinan babban sakataren ma’aikatar, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, da zarar an kammala Shari’un da masu kayan za’a ƙone su baki ɗaya.

“A bisa al’adar ma’aikatar ciniki da masana’antu, dama duk sabon Kwamishina idan ya zo yana ziyarartar hukumomin da suke da jiɓi da ma’aikatar domin duba irin aikace-aikacen su da sauran abinda ba’a rasa ba, hakan ya sa ma Kwamishinan ya ziyarci hukumar a yau, “in ji Ɗan-duwa”.

 

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, babban sakataren ya ƙara da cewa, ziyarar da Kwamishinan ciniki da masana’antun Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kai hukumar kula da ingancin kayayyakin, itace ta farko.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Trending